A wata sanarwar bayan taro da gamayyar kungiyoyin kadago na kasar nan suka fitar ranar Talata, NLC ta ce kaf din su kungiyoyin Kwadago na kasar nan za su fara yajin aiki na gamangari daga ranar 3 ga Oktoba.
Kungiyar ta ce gwamnatin tarayya da na jihohi sun yi biris da su sannan kuma har yanzu basu cika alƙawuran da suka ɗauka ba a kasar nan.
Daga wannan ranar 3 ga Oktoba, duk wani ma’aikaci a ƙasar nan ba zai je aiki ba, zai shiga cikin wannan yajin aiki gadangadan.
Sannan kuma mun umarci duka kungiyoyin mu da ma’aikata tun daga gwamnatin tarayya da zuwa kananan hukumomi, su fara shirin zanga-zanga gadan gadan tin daga yanzu, domin daga wannan rana wato Talata, 3 ga wata, ruf zamu rufe kasar nan, babu aiki, babu makaranta, babu wuta, babu ruwa, babu, komai sai gwamnati ta saurare mu ta biya mana bukatu.
Mun lura cewa da gangar gwamnatin Tinubu ba ta da niyyar kawo karshen tsananin wahala da ta tsinduma ƴan Najeriya a ciki. Sun kama gaban su ba bu abinda ya dame su
Kungiyar ta ce hakan ba zai saɓu ba. Ko dai a saurare su a kawo saukin wahalar da aka saka mutane ciki ko kuma a fara yajin aikin da babu ranar gama shi.
Sai dai kuma har yanzu, gwamnatin Najeriya ƙarƙashin ministan Kwadago ‘, Simon Lalong, ta roki NLC ta ba gwamnati dama da ƙarin lokaci domin wanye matsaloli da buƙatun NLC ɗin.
Haka shima kakakin majalisar Tarayya, Abbas, ya roki kungiyoyin su maida wuƙaƙen na su, cewa lallai gwamnati na duba korafe korafen na su kuma za a samu tsaya ɗaya nan ba da dadewa ba
Discussion about this post