Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT) Abuja, Nysome Wike, ya tabbatar da cewa zai yi ba-sani-ba-sabo wajen rushe duk wani gini da aka yi ba bisa ƙa’ida ba a Abuja.
Haka dai ya jaddada a cikin wani sabon bidiyon sa, wanda aka watsa a ranar Juma’a.
Wike ya yi wannan gargaɗin mako ɗaya bayan yaɗa wani bidiyon sa, inda aka nuno shi ya na gargaɗin cewa ba zai bari a riƙa kafa rumfar laima ana ‘yan saide-saiden kayayyaki a gefen titinan Abuja ba.
A cikin sabon bidiyon, wanda bai wuce minti ɗaya ba, an nuno Wike ya na cewa:
“Duk wanda ya yi gini a shacin wuraren shaƙatawa masu bishiyoyi (green areas), to za mu rushe shi. Ginin ko ma na wane ne sai ya je ƙasa.
“Ko kai Minista ne ko Jakada, idan ka yi gini a wurin da ba a ce a yi gini ba, ko kuma ka yi gini ba bisa ƙa’ida ba, zan rushe shi.”
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin da Minista Wike ya ce zai fatattaki masu kasa kaya gefen titi da masu karakainar tallace-tallace.
A cikin labarin, Ministan Babban Birnin Tarayya, FCT Abuja, Nysome Wike, ya sha alwashin cewa zai fatattaki duk masu kasa kaya gefen titi a cikin Abuja su na ‘yan saide-saiden kayayyaki.
Cikin wani faifan bidiyon da ke yawo a soshiyal midiya, an nuno Wike ya na cewa, “ba zan amince haka kawai a zo ana kafa laima gefen titi a cikin Abuja ba, ana wasu harkokin kasuwanci.
“Babban aiki na shi ne tabbatar da wanzuwar zaman lafiya da bunƙasa Abuja. Ba a gina Abuja don a riƙa tallace-tallace da saide-saiden kayayyaki barkatai ba.
“Ina mamakin yadda za ka ga mutum ba a san daga inda ya ke ba, ya zo ya kafa ‘yar rumfar laima (umbrella) a gefen titi, wai ya na sayar da kayayyaki. To wannan barazana ce ga mazauna Abuja.
“Saboda irin su infoma ne na ‘yan fashi. Su na zaune ƙarƙashin ‘yar laima duk su na lura da shige-da-ficen masu gidaje. Ka na shiga gida sai dai ka ji sun kira ‘yan fashi, sun ce mutumin fa ya dawo, ya shiga gida yanzu.” Inji Wike a cikin bidiyon.
Discussion about this post