Kotun sauraron kararrakin zaben Sanatan Kogi ta Gabas a ranar Talata ta kori sanata mai wakiltar gundumar, Jibrin Isah, saboda an soke zabe a rumfunan zabe 94.
Kotun ta kuma umarci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da ta gudanar da zabe a rumfunan zabe 94 da abin ya shafa.
Babban Alkalin kotun, K.A. Orjiako, wanda ya yanke hukunci kan karar da dan takarar jam’iyyar PDP Victor Adoji ya gabatar a gabanta a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu, ya amince da ƙorafin Adoji.
Adoji ya kalubalanci sakamakon zaɓen da hukumar zaɓe ta bayyana a lokacin cewa bayan an lissafa duka ƙiri’un da aka kaɗa, an samu batattun kuri’u da aka karbi katin zaɓen su da sun fi yawan kuri’un da ɗan takarar APC ya yi nasara da su.
A dalilin haka ya nemi kotu ta soke zaɓen sai an koma an yi zaɓe a rumfunan zaɓe 94, sannan ne za a iya sanin wanda ya yi nasara a zaɓen.
Bisa hujjojin Da Lauya Adoji ya bada a gaban kotu, Alkalin kotun ya soke wannan zaɓe sannan ya umarci INEC ta sake gudanar da zaɓe a rumfunan da aka soke.
Tunda sakamakon zabe da aka tattara a rumfunan zabe 94 ya kai 59,730, yayin da tazarar da aka samu shine kuri’u 26,922, ya kamata jami’in zaben ya bayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba tun farko, maimakon yin gaban kansa ya bayyana wani a matsayin wanda ya yi nasara.
Discussion about this post