Kotun sauraren ƙararrakin zaɓen gwamnan Kaduna ta yi watsi da shari’ar PDP da ta ƙalubalanci nasarar da Uba Sani na APC ya yi a zaɓen 28 ga Maris.
A hukuncin da kotun ta yanke, ta ce wai PDP da ɗan takaran ta Isah Ashiru ba su shigar da kara akan lokaci ba.
Shugaban kotun ya ce, PDP da ɗan takaran ta Ashiru ba su shigar da kara a kwanakin da doka ta gindaya tun farko ba. Jakan ya sa idan aka yi dubi da ita kanta gundarin shari’ar ba kau matsayin a saurare ta ba ballantana a ce za a yanke sahohiyar hukunci a kan ta.
Sai dai kuma Kotun ta ce da ba don wannan tsautsayi da PDP ta tsindima ciki ba, da kotun za ta yanke hukuncin rashin kammalar zaɓen ne wato ‘Inkonclusib’
” Kotu za ta yanke cewa zaɓen gwamnan bai kammala ba, sannan kuma hukumar zaɓe ta sake zaɓe a wasu mazabu cikin kwanaki 90.
Gwamna jihar Uba Sani, ya yi murnar nasarar da ya samu a shari’ar yana mai cewa ” an tabbatar wa mutanen Kaduna abinda suka zaɓa ne a watan Maris.
” Ina mai godewa mutanen Kaduna da kuna jinjina wa alkalan da suka yanke wannan hukunci da kuma nasarar da na samu. Wannan nasar da na samu a Kotu nuni me cewa lallai jama’ar Kaduna na tare da mu a wannan tafiya.
Discussion about this post