Kotun sauraren kararrakin zabe na kujerar majalisar Dattawa na Kaduna ta Tsakiya ta yanke hukunci a kan karar da Muhammad Sani Dattijo ya shigar inda yake kalubalantar nasarar Sanata Lawal Adamu Usman (Mr LA) a zaben 25 ga watan Faburairun 2023.
Kotun ta yi watsi da karar da Muhammad Sani Dattijo ya shigar inda Alkalan kotun su ka ayyana cewa zarge-zargen da shi mai kara ya shigar bai iya gamsar da kotu da kwararan hujjoji ba, hasali ma, zarge zargen ba su da tushe ballantana makama.
Hakan yasa kotun ta kara tabbatar da nasarar Sanata Lawal Adamu Usman (Mr LA) a matsayin halastaccen sanata mai wakiltan Kaduna ta Tsakiya a majalisar Dattawa.
Alkali HH Kereng ya bayyana cewa duka korafin da Dattijo ya mika wa kotu, ya kasa ba da sahihan hujjoji da za su gasgata abubuwan da yake korafi a kai.
” Dattijo ya kasa kawo mana sahihan hujjoji da za su gamsar da kotu, kame-kame kawai ya rika yi, da kawo hujjojin da basu da tushe ballantana makama.
” A dalilin haka ne kotu ta yi watsi da wannan kara.
Ƴaƴan Jam’iyyar PDP sun rila kida su na tika rawa a garin Kaduna domin nuna farncikin su ga wannan nasara da gwanin su ya samu a kotu.
” Wannan nasara ce daga Allah, kuma muna mika cikakkiyar godiyar mu ga Allah bisa tabbatar mana da cikakkiyar nasara tare da rinjaye a wannan Shari’ar. Muna rokon Allah Ya taimaki Sanata Lawal Adamu Usman (Mr LA), Allah Ya ba shi kariya, hikima da basirar gudanar da aikin al’ummar Kaduna ta Tsakiya.”
Sai dai kuma Dattijo da jam’iyyar sa APC ba su ce komai ba akan wannan hukunci. Wani makusanci ɗan takarar ya shaida wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa za su duba hukuncin kotun daganan sai su bayyana matsayar su.
Discussion about this post