A ranar Litinin ne Kotun majistare dake Iyaganku a Ibadan ta yanke wa wani Olaniyan mai shekaru 30 hukuncin zaman kurkuku na tsawon watanni shida bayan an kama shi da wasu sassan jikin mutane.
Alkalin kotun T . G. Daudu ta ce Olaniyan zai yi zaman kurkuku tare da yin aiki mai tsanani saboda laifin da ya aikata.
Kotu ta yanke wannan hukunci ne bayan Olaniyan ya amsa laifin sa.
Lauyan da ya shigar da karar Folake Ewe ya ce an kama Olaniyan ranar 3 ga Satumba da misalin karfe 3:10 na dare.
Ewe ya ce jami’an tsaro sun kama Olaniyan a makabartar dake hanyar Eruwa zuwa Igboora bayan ya hako wani gawa ya cire kai da wasu sassan jikin gawar.
Ya ce mutumin ya aikata wannan laifi tare da taimakon matarsa mai suna Modina sannan zuwa yanzu ‘yan sanda na neman ta ruwa a jallo.
Ewe ya ce kungiyar ‘yan sa kai da mafarauta ne suka kama Olaniyan.
Discussion about this post