Kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa ta tabbatar da Bola Tinubu a matsayin sahihin zababben shugaban kasar Najeriya.
Haruna Tsammani, shugaban Alkalai biyar na kotun da ya yanke hukuncin, ya bayyana hakan bayan watsi da karar Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP.
Shari’ar Atiku ita ce ta uku kuma ta karshe daga cikin kararrakin, da ke ƙalubalantar nasarar da Tinubu y na APC ya yi a zaɓen 25 ga watan Fabrairu, da kotun ta yi watsi da shi a hukuncin da ta yi na tsawon sa’o’i 12 a ranar Laraba.
A baya dai kotun ta yi watsi da karar da Peter Obi na jam’iyyar Labour Party da All Peoples Movement (APM) suka shigar.
Korafe-korafe guda uku da ake zargin Tinubu ya yi sun haɗa da rashin cancantar tsayawa takarar shugaban kasa, da rashin bin ka’ida da yin aringizo da cuwacuwa a lokacin zaben, da kuma gazawar Tinubu wajen cika cikakkun sharuddan da kundin tsarin mulkin kasar ya gindaya na a ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben saboda gazawarsa na samun kashi 25 cikin 100 na kuri’un da aka kada a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.
A hukuncin Kotu ta ce duka hujjojin da masu shigar da kara suka bayyana a gaban ta ba su gamsar da kotu ba.
Discussion about this post