A ci gaba da samun nasara da jam’iyyar APC ke yi a shari’ar zaɓukan kujerun ƴan majalisan tarayya na Kano, a ranar Asabar, APC ta samu nasarar kwace kujera ɗaya.
A hukuncin da Alkalin kotun ya yanke kan ƙarar da Musa Kwankwaso na APC ya shigar yana ƙalubalantar nasarar da Ahmed Datti na NNPP ya samu a zaɓen Faburairu kotu ta ce Kwankwaso ne zaɓaɓen wakilin Kura/ Madobi/ Garùn-Malam a majalisar Tarayya ba Yusuf Datti ba.
Kwankwaso na kalubalantar nasarar Datti ta hanyar karya dokar zaɓe da ya ce ya yi.
A hukuncin da kotu ta yanke, ta umarci hukumar Zaɓe ta janye satifiket din da ta ba Datti, ta mika wa Kwankwaso.
Alkali ya ce an gano ashe Datti bai ajiye aiki da ya ke yi a jami’ar BUK ba kwanaki 30 da kafin zaɓe ba kamar yadda doka ta gindaya. Wannan shine dalilin da ya sa kotu ta kwace kujerar domin karya wannan doka da ya yi.
Discussion about this post