Kotun sauraren kararrakin zabe ta Majalisar Dokoki ta kasa da ta Jiha da ke zamanta a Kano ta amince da zaben Kawu Sumaila na jam’iyyar NNPP mai wakiltar mazabar Kano ta Kudu.
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana Sumaila a matsayin wanda ya lashe zaben Sanatan Kano ta Kudu da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.
Sanata Sumaila ya lashe zaben Sanata ne da kuri’u 319,557. Ya ka’da Kabiru Gaya na jam’iyyar APC wanda ya samu kuri’u 192,518.
Dan takarar APC, Gaya, ya kalubalanci nasarar Sumaila a kotun sauraron kararrakin zabe.
A ranar Litinin ne kotun ta yi watsi da karar da Gaya ya shigar kan rashin cancantarsa da kuma cin shi tarar N200,000 ya baiwa sanata Sumaila ya sha ruwa na bata masa lokaci da ya yi a kotu.
Shugaban kotun, R. Odogu, ya ce wanda ya shigar da karar ya kasa bada sahihan hujjoji da za su gamsar da kotun.
Discussion about this post