Kotun majistare dake Gwagwalada a Babban Birnin Tarayyar Najeriya, Abuja ta belin Rabiu Moyi mai shekara 20 kan naira 200,000 bisa zargin da yake yi cewa wani ya sace masa azakari.
Alkalin kotun N.A. Tukur ya ce Moyi dake zama a Wazobia Park dake Dagriri Gwagwalada zai gabatar da shaidu biyu dake zama a wurin da kotun ke da iko.
Tukuru ya ce shaidun za su gabatar da takardan shaidar biyan wutan lantarki ko ruwan fanfo sannan da lambar katin zama dan kasa.
Ya ce za a ci gaba da shari’a ranar 29 ga Oktoba.
Lauyan da ya shigar da kara Abdullahi Tanko ya ce wani Timothy Saa dake zama a Suleja jihar Niger ya kawo da kara ofishin ƴan sanda ranar 20 ga Satumba.
Tanko ya ce a wannan rana Moyi ya ce Saa da abokansa sun lakada masa dukan tsiya da garin dukan ne suka sace masa a zakari.
“Moyi ya ce ya ji rauni a idonsa da hannunsa sannan har ya yi jinya a asibiti a dalilin dukan da ya sha.
Lauyan ya ce Moyi bai iya bada gamsasshiyar bayani ba a gaban jami’an tsaro kan yadda aka sace masa azakari.
Dalilin haka ne ya sa kotu ta hukunta shi domin hakan ya zama darasi ga na baya.
Discussion about this post