Cibiyar gwada asalin kwayoyin halitta ‘Smart DNA’ dake jihar Legas ta gabatar da sakamakon gwajin da ta yi wa mutane daga Yuli 2022 zuwa Yuni 2023.
Bisa ga sakamakon gwajin da cibiyar ta gabatar mutum kashi 73.88% sun samu tabbacin sune mahaifan ‘yan da suke zaton ba ‘ya’yan su bane sannan kashe 26.13% sun gano cewa ‘ya’yan da suke zaton ‘ya’yan su ne ba ‘ya’yan su bane.
Sakamakon ya kuma nuna cewa mutane a jihar Legas sun fi yin wannan gwajin wa ‘ya’yan su inda a jihar kashi 82.89 ne suka yi wa ‘ya’yan su gwajin.
Daga nan sai jihar Oyo kashi 3.29%, Ogun kashi 3.07%, Babban Birnin Tarayya Abuja kashi 2.63% da Rivers kashi 2.41%.
“A jihar Legas mazaunan Mainland kashi 68.14% ne suka gwada asalin kwayoyin halittar ‘ya’yan sannan kashi 31.86 na mazan dake zama a Island.
“Cibiyar na tsammanin mazan dake Mainland sun fi gwada ‘ya’yan su saboda mafi yawan mazauna wurin attajirai ne fiye da wadanda ke zama a Island sannan kuma ofishin cibiyar a Main land yake.
Cibiyar ta bayyana cewa kashi 89.10% sun yi wa ‘ya’yan su gwajin domin samun kwanciyar hankali, kashi 8.97% saboda samun takardun dan kasa, kashi 0.64% saboda umarnin kotu.
Maza kashi 86.44% ne suka fi zuwa cibiyar domin yi wa ‘ya’yan su gwajin fiye da mata kashi 13.56%.
Daga nan cibiyar ta nuna cewa an fi auna ‘ya’ya maza masu shekara 0-5 fiye da ‘ya’ya mata masu shekara 6-12.
Maza masu shekaru 31-40 da shekaru 41-50 ne suka fi yi wa ‘ya’yan su wannan gwajin.
Discussion about this post