Wata matar aure Jamila Momoh a ranar Laraba ta garzaya kotun Grade 1 dake Kubuwa a Abuja inda ta nemi kotu ta raba auren ta da mijinta Suleiman Shazaliyu saboda rashin kula.
Jamila da Shazaliyu na da ‘ya’ya hudu.
Ta ce tun bayan auren su auren Shazaliyu ya yi watsi da ita.
“Tun bayan auren mu Shazaliyu ya daina kula da ni baya ma saduwa da ni a matsayin matarsa ta aure.
“Iyaye da abokan mu sun yi kokarin sasanta mu amma abin ya ci tura.
Shazaliyu bai halarci zaman kotun ba sannan shi rajistaran kotun Dangana Bawa ya ce ya kira shi ta waya amma duk da haka ya ki zuwa.
Lauyan dake kare Jamila, Otacha Bako ya roki kotn da ta kara aikawa mijin sammace.
Alkalin kotun Malam Ibrahim Rufai ya bada umarnin a kara aika wa Shazaliyu sammace, daga nan sai ya dage shari’ar zuwa 19 ga Satumba.
Discussion about this post