Akalla ɗaliban jami’ar gwamnatin Tarayya dake Gusau ne ƴan ta’adda suka sace a hari da suka kai wa ɗaliban a daren Alhamis.
Wani da ya zanta wa wakilin PREMIUM TIMES a Gusau ya shaida cewa ƙanwar sa ta tsira da kyar ba a waske da ita ba.
Sai dai kuma an ceto wasu ɗalibai shida da aka yi garkuwa da su.
AbdulMalik ya ce kanwar sa ta shaida masa cewa da maharan suka dira Sabon Gari, sun rika shiga gida-gida ne suna kwashe ɗalibai.
Saboda ƙarfin hali da samun wuri, ƴan bindigogin ga sun tare hanyar Gusau zuwa Funtua sannan suka ajiye wasu mahara a kofar shiga jami’ar.
Sai dai bayanai sun nuna cewa jami’an tsaro sun fantsama cikin daji domin dawo da ɗaliban da aka sace.
Rahotanni dun nuna cewa kafin harin, ƴan bindiga sun rika yi wa ɗaliban ɗauki ɗaiɗai.
Discussion about this post