Tsohon shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya jinjina wa kotun shari’ar zaben shugaban kasa da alakalai biyar da suka yanke hukuncin da ya tabbatar da Bola tinubu wanda ya yi nasara a zaben shugaban kasa na Faburairu.
A sakon murna da wannan hukunci, Buhari ya ce ” Ya dai kamata a maida wukaken yanzu a dawo a hada kai domin ci gaban kasa tunda hukuncin kotu ya tabbatar wa Tinubu nasarar da yayi a watan Faburairu.
” Ina kira ga ‘yan Najrtia su ba wannan gwamnati goyon baya domin a samu nasara kan abin da aka sa a gaba.
Atiku ya garzaya kotun Koli
Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi watsi da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa (PEPC) ta yanke, inda ta tabbatar da zaben shugaban kasa Bola Tinubu, yana mai cewa “ba a yi adalci ba.”
Atiku ya ce ya umarci Lauyoyin sa su garzaya kotun Koli, a je can a fafata.
” Hukunci ne da ba zan yarda da shi ba. Na ƙi yarda da hukuncin saboda na yi imani cewa ba a yi adalci ba. Sai dai rashin jin dadin hukuncin da kotu ta yanke ba zai sa in yanke kauna da kotun Najeriya ba. Na tabbatar za su yi mani adalci a gaba.
A dalilin haka na umarci Lauyoyi na su garzaya kotun koli. Ba za mu yarda a bari ana murdiya a zabukan kasar nan sannan muzuba ido mu bari ba. Za mu can kotun koli mu fafata, kuma mau karbo nasarar mua a can.
Atiku ya ce ko yayyi nasara ko bai yi ba, ya tabbata zai shiga cikin tarihi cewa ya taka rawar gani don tabbatar da dimokradiyya sahihiya wanda za a rika alfahari da ita a kasar nan.
Haka shima dan takarar LP, Peter Obi, ya garzaya kotun Kolin domin kalubalantar hukuncin kotun shari’ar zaben shugaban kasa. Obi da Atiku duk sun ce suna suka yi nasara a zaben shugaban kasa da aka yi awatan Faburairu ba Tinubu ana APC ba.
Discussion about this post