Hukumar Kwastam NCS dake kula da shiyar Kano da Jigawa ta bayyana cewa hukumar ta tara naira biliyan 28.8 daga Janairu zuwa Agusta.
Kwamandan shiyar mai barin gado, Sambo Dangaladima, ya bayyana haka a lokacin da yake mika wa sabon Kwanturola da zai maye gurbin sa Dauda Ibrahim Chana a Kano ranar Laraba.
Dangaladima ya ce a hukumar ta maida hankali matuka wajen tara har naira biliyan 5.1 a watan Agusta.
Ya ce hukumar ta kama kayan da gwamnati ta hana shigowa da su da kudin su ya kai naira miliyan 248 a cikin watanni 8.
Dangaladima ya ce hukumar za ta ci gaba da za Ido domin ganin ta hana shigo da kayan da gwamnati ta hana.
Ya kuma hori jami’an hukumar da su mara wa sabon kwamandan shiyar domin inganta hukumar.
A nashi tsokacin sabon kwamandan hukumar Ibrahim Chana ya ce zai yi aiki tukuru domin ganin hukumar ta hana shigo da kayan da gwamnati ta hana.
Discussion about this post