Hukumar Kwastam reshen jihar Ogun ta bayyana cewa jami’an ta sun kama haramtattun kaya da kuɗin su ya kai naira biliyan 6.6. a cikin watanni 17 a jihar.
Shugaban hukumar Bamidele Makinde, ya sanar da haka a wata takarda dake dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar Hameed Oloyede ranar Alhamis.
Makinde ya ce haramtattun kayan da jami’an hukumar suka kama sun hada da buhunan shinkafa 73,989, belin kayan gwanjo na sawa 907, da wasu kayan ɗaure a buhuna 236.
Saura sun hada da man fetur lita 655,400, harsasai 1,245 da ɗaurin ganyen wiwi guda 2,678
A lisaffe dai kudin kayan da hukumar ta kama ya kai naira biliyan 6,604,107,655.92.
Discussion about this post