Wasu Shugabannin Jami’o’i sun bayyana a gaban Kwamitin Binciken Harƙallar Ɗaukar Ma’aikata, inda su ka yi rantsuwar kaffara cewa sun yi wa ‘yan kwamitin ƙaryar cewa sun ba su kuɗaɗe.
Rantsuwar kaffarar dai wani shiri ne na binne gadangarƙamar karɓar kuɗaɗen da ‘yan kwamitin su ka yi a hannun shugabannin jami’o’in.
PREMIUM TIMES ce ta fallasa yadda ‘yan kwamitin su ka karɓi kuɗaɗe a hannun shugabannin cibiyoyi, hukumomi da ma’aikatun gwamnati.
Kowanen su ya tura masu Naira miliyan 2 a asusun Bankin Providus Bank.
Shugaban Kwamitin Bincike, Yusuf Gagdi ne ya gayyaci Shugabanin Jami’o’in a yau Juma’a, domin yin bayani kan labarin da PREMIUM TIMES ta buga.
Kimanin Shugabannin Jami’o’i 10 ne da kuma Sakataren Riƙo na Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC), Chris Maiyaƙi, su ka bayyana gaban Kwamitin Bincike a Majalisar Tarayya, a yau Juma’a.
Gagdi ya maimaita cewa wannan jarida ta yi binciken ƙarya ce kawai don ta karkatar da kwamitin daga aikin binciken da ya ke yi.
Amma kuma lokacin da ya ce Shugabannin Jami’o’in da Maiyaƙi su yi magana, bai ce su rantse ba.
Sai ya ce masu rantsuwar da su ka yi a can baya a gaban kwamitin ta wadatas.
Da ya ke bayani, Maiyaƙi bai taɓo batun hujjojin da PREMIUM TIMES ta buga cewa an biya kuɗaɗe ga ‘yan kwamiti ta cikin Asusun Providus Bank ba.
Maimakon haka, sai Maiyaƙi ya ce Shugaban Jami’ar Jos, Ishaya Tanko ya yi bayani a madadin sauran shugabannin jami’o’in.
Tanko ya ce ‘yan Majalisa ba su nemi kuɗi a hannun su ba. Sannan ya soki PREMIUM TIMES saboda a cewar sa, ba ta tuntuɓe su ba kafin ta buga labarin.
Sai dai kuma ya manta cewa PREMIUM TIMES ta buga cewa ta tuntuɓi Shugabar Ƙungiyar Shugabannin Jami’o’in Najeriya (CVCNU), Lilian Salami, sai kuma ɗaya Shugaban CVCNU ɗin, kuma Shugaban Jami’ar Bayero ta Kano.
An kira su ba su ɗauka ba, kuma an yi masu saƙon tes, duk su ka ƙi bada amsa.
Tanko ya tabbatar wa kwamitin cewa Shugabannin Jami’o’i sun zuba kuɗaɗen kamar yadda PREMIUM TIMES ta bayyana a cikin asusun Providus Bank.
Sai dai kuma ya ce, “kuɗaɗen ba rashawa ba ce ga ‘yan majalisa. Ya ce kuɗaɗe ne su ka tattara domin su sayi Dala domin halartar wani taron da wasu Shugabannin Jami’o’i za su je.”
Tanko bai faɗi sunan taron ba, ya dai ce a Birmingham za a yi taron. Daga nan ya waske.
“A Birmingham, ƙasar Ingila za a yi taron. Wasu gobe za su tafi, wasu kuma sai jibi. Saboda ranar Talata mai zuwa za a fara taron horaswar a Birmingham.” Inji Tanko.
Wata Sabuwa: Tanko Da ‘Yan Kwamiti Tantiran Maƙaryata Ne – PREMIUM TIMES:
Dangane da wannan asarƙala, PREMIUM TIMES ta ma ƙara tabbatar da binciken da ya ƙara nuna Tanko tantirin maƙaryaci ne, har ma da su kan su ‘yan Kwamitin Bancike.
Za mu kawo maku cikakken rahoton yadda kwamitin a ƙarƙashin Yusuf Gagdi ya samo ‘kamfanin ‘yan canji’ na AMA Business Solutions, wanda Shugabannin Jami’o’i su ka riƙa tura masu kuɗaɗe a ciki.
Ku ɗan saurare mu, domin ki ji komai.
Majalisar Tarayya za ta binciki Kwamitin Binciken Harƙallar Ɗaukar Ma’aikata, bayan PREMIUM TIMES ta fallasa cuwa-ciwar da kwamitin ke karɓa a hannun shugabannin
hukumomin gwamnatin tarayya.
Majalisar Tarayya ta tabbatar da cewa za ta binciki Kwamitin Binciken Harƙallar Ɗaukar Ma’aikata, bayan PREMIUM TIMES ta fallasa cuwa-ciwar da kwamitin ke karɓa a hannun shugabannin hukumomin gwamnatin tarayya.
Binciken wanda ya ɗauki PREMIUM TIMES makonni ta na gudanarwa, ta fallasa yadda ‘yan majalisa ke yi wa shugabannin hukumomi, cibiyoyi da na ma’aikatun gwamnatin tarayya barazana, su na karɓar kuɗaɗe a hannun su, don su wanke su daga harƙallar ɗaukar ma’aikata ba bisa ƙa’ida ba.
Bayan rahoton na PREMIUM TIMES ta fusata ‘yan Najeriya da dama kan ‘yan majalisa, Kakakin Yaɗa Labaran Majalisar Tarayya, Aikin Rotimi ya fitar da sanarwa a ranar Talata cewa Majalisa za ta binciki batun.
Sai dai Rotimi bai bayar da sanarwar yadda majalisar za ta yi binciken ba, sai dai ya ce “duk wani mai wata shaida ko da kuwa ma’aikacin gwamnati ne, to ya gabatar wa Majalisa shaidar sa, domin ta ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki.”
Sai dai kuma Rotimi ya ce kwamitin na fama da yadda mutane su ka ɗora masa karan-tsana saboda aikin da ya ke yi.
Yadda PREMIUM TIMES Ta Tallasa Cuwa-cuwar Kwamitin Binciken Harƙallar Ɗaukar Ma’aikata:
Kowane Gauta Ja Ne: Yadda ‘Yan Kwamitin Majalisa masu Binciken Harƙallar Daukar Ma’aikata ke karɓar rashawa da toshiyar-baki daga Shugabannin Ma’aikatun Gwamnati:
Wani binciken ƙwaƙwaf da PREMIUM TIMES ta gudanar ya fallasw yadda ‘Yan Kwamitin Majalisa masu Binciken Harƙallar Daukar Ma’aikata ke karɓar rashawa da toshiyar-baki daga Shugabannin Ma’aikatun Gwamnati tsawon makonni da dama.
Binciken ya gano daga cikin shugabannin cibiyoyi da ma’aikatu da hukumomin da su ka riƙa tumbuza masu kuɗaɗe a wani asusun banki, har da shugabannin makarantun gaba da sakandare.
Kwamitin dai ya shafe kwanaki ya na gayyatar shugabannin cibiyoyi, hukumomi da ma’aikatun gwamnatin tarayya ana yi masu titsiye da fallasar yadda su ke ɗaukar ma’aikata ba bisa ƙa’idar da doka ta shimfiɗa ba.
Cikin hukumomin da aka titsiye har da Hukumar Jarabawar Shiga Jami’a Farfesa Ishaq Oloyede da Shugabar Hukumar Daidaiton Ɗaukar Ma’aikata ta Ƙasa, Khadija Ɗankaka.
‘Yan cuwa-cuwar mambobin Majalisar dai su 39 ne a cikin kwamitin, kuma an naɗa su tun a ranar 5 Ga Yuli.
An ɗauko mamba ɗaya daga cikin mambobin kowace jiha da kuma Abuja, sannan aka naɗa Yusuf Gadgi matsayin Shugaban Kwamiti. Gagdi na wakiltar Jihar Filato ne, kuma ɗan APC ne.
Sai dai kuma Oluwole Oke wanda ya bada shawarar a kafa kwamitin, kwata-kwata ko sunan sa babu a cikin mambobin kwamitin binciken.
Yayin da ɗimbin ‘yan Najeriya ke ta murnar kafa kwamitin, ganin yadda aka riƙa danne wa dubban ‘yan Najeriya damar samun aiki, ashe ba a sani ba kwamitin binciken ba kankare ba ne, tubalin toka ne.
Ashe duk barazanar da zare idanun da mambobin kwamitin ke yi a zauren bincike, duk talakawa ake raina wa wayau, ana kuma bagaras da su.
Yayin da ake yi wa shugabannin hukumomi, cibiyoyi da ma’aikatun gwamnati mazurai duniya na kallo a talbijin, da sun kulle ƙofa a tsakanin su kuma sai a kama cinikin yadda za a bai wa ‘yan kwamitin toshiyar baki, tsakanin ‘yan kwamiti da shugabannin na cibiyoyi, ma’aikatu da hukumomi.
Misali, a ranar 15 Ga Agusta, wasu mambobin kwamitin sun gana da Shugabannin Jami’o’in Gwamnatin Tarayya 51, aka umarci kowanen su ya biya Naira miliyan 3 don kada a tozarta shi a zauren bincike.
Farfesoshin dai sun yi ƙememe su ka ce ba za su biya ba, domin wasun ma makarantun ma su da cibiyoyi ko kuɗaɗe gwamnatin ba ta ba su wadatattu.
Daga nan aka rage farashi zuwa Naira miliyan biyu kowanen su zai bayar.
Daga nan aka bai wa kowane Farfesa akawun lamba 5400495458 ta Bankin Providus Bank, aka ce kowa ya zuba miliyan biyu a ciki.
Saboda tsabar rashin kunya har mambobin kwamitin su ka ce kowane shugaban jami’a ya rubuta sunan makarantar sa a wurin tura kuɗaɗen.”
Bayan nan kuma kwamitin ya yi ganawa da shugabannin manyan Kwalejojin Fasaha na gwamnatin tarayya 35, sai kuma wata ganawar da shugabannin Kwalejojin Ilmi mai Zurfi su 27, aka nemi kowanen sa ya biya miliyan 3, don kada a kunyata shi a gaban kyamara da ɗimbin ‘yan jarida masu haskaka ana kallo.
PREMIUM TIMES ta gano manyan makarantu sun biya jimillar naira miliyan 267, kuma Mambobin sun kwashe kuɗaɗen.
Hakan na nufin a lokacin da za su gama binciken cibiyoyi, ma’aikatu da hukumomi 1,500, kuɗaɗen da mambonin kwamitin binciken za su samu, za su iya tara biliyoyin nairori.
PREMIUM TIMES ta gano cewa asusun da aka riƙa tura kuɗaɗen mallakar Ama Business Solutions ne.
Kamfanin an kafa shi ranar 12 Ga Agusta, 2020, ya na da lasisin rajista mai lamba 3156889.
Adireshin sa shi ne Lamba 2249, Zone 4 Plaza, Titin Constantine, Wuse 4, Abuja.
Kamfanin na wasu mutum biyu ne, Abubakar Lawal Sambo da Abdulrahman Lawal Sambo.
Su biyun sun nuna cewa ‘yan kasuwa ne, amma Abdulrahman ya taɓa zama Hadimin tsohon Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila.
Discussion about this post