Hukumar Tsaro ta SSS sun damƙe Mataimakiyar Gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, A’isha Ahmed.
An kama ta ne dangane da hannun da ta ke da shi wajen yadda aka bi bauɗaɗɗiyar hanyar danƙara hannayen jari a bankunan Polaris Bank da Titan Bank, wato Union Bank na da.
Aisha Ahmad ita ce Mataimakiyar Gwamnan CBN mai lura da yawan kuɗaɗen hada-hada a bankuna.
Gidan Talbijin na NTA ya ruwaito kama ta, tare da cewa ta na da hannu wajen yadda aka kqmfaci Dala miliyan 300 a asirce aka sayi hannayen jari da Polaris Bank da Titan Bank, wato Union Bank a da.
“SSS na binciken Mataimakiyar Gwamnan CBN dangane da hannun da ta ke da shi wajen yadda aka kamfaci Dala miliyan 300 aka cikasa Kuɗaɗen sayen hannayen jarin da Titan Bank ya saya a Union Bank.”
Har yanzu dai SSS da CBN ba su ce komai ba dangane da kama A’isha da aka yi.
Har yanzu dai shi ma tsohon Gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya na tsare a hannun SSS.
Cikin watan Agusta kuma PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa wata ma’aikataciyar CBN mai suna Sa’adatu Yaro, wadda ake zargin harƙallar Naira Biliyan 7 tare da Emefiele, ta na fuskantar wata tuhumar walle-wallen Naira biliyan 140.
A cikin wancan labarin, wannan jarida ta buga cewa Sa’adatu Yaro, wadda ake zargin harƙallar Naira Biliyan 7 tare da Emefiele, ta na fuskantar wata tuhumar gada-gada daban a wata kotun, tun ma kafin a kai ga kama tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.
EFCC sun damƙe ta sannan suka gabatar da ita a Babbar Kotun Tarayya ta Abuja, a gaban Mai Shari’a Obiora Egwuatu, bisa tuhumar neman Naira biliyan 140 a hannun ta.
An gurfanar da ita tare da kamfanin ta mai suna Tsami Babi Resources Limited, saboda laifin ƙin bayyana wa Ma’aikata Cinikayya cewa kamfanin na ta ne, duk kuwa ita Darakta ce a kamfanin.
Tuhume-tuhumen Da Ake Wa Sa’adatu Ramallan Yaro:
“A matsayin Sa’adatu Ramalan Yaro a matsayin ta na Daraktar Tsami Babi Resources Limited, an narka wa kamfanin ta Naira biliyan 20.9, Naira a asusun kamfanin mai lamba 1216254641 na Zenith Bank.
“An tura kuɗaɗen a ranakun 5 Ga Yuli, 2021, sai kuma 20 ga Afrilu, 2021.
A wata tuhumar kuma, ana cajin ta tare da wani kamfani M.A.Y Limited, sun karkatar da Naira biliyan 40.
Lokacin da aka gabatar da ita, lauyan ta Joseph Daudu, ya nemi a bayar da belin ta, inda daga nan dai Mai Shari’a ya bada belin ta a kan kuɗi Naira miliyan 100. Sai kuma masu karɓar beli mutum biyu.
Mai Shari’a ya ce tilas ɗaya mai belin ya kasance ma’aikacin gwamnatin tarayya, ɗaya kuma zai kasance ɗan’uwan ta ne.
Sannan aka umarci ta bayar da fasfo ɗin ta na fita waje a kotun sa, wurin Babban Rajistara.
Kafin wannan kuma, an gurfanar da ita a Babbar Kotun Tarayya da ke Legas, a kan zambar kuɗaɗe. Sa’adatu dai ma’aikaciyar CBN ce.
Discussion about this post