Tsohon Ministan Makamashi da Ƙarafa, Olu Agunloye, ya zargi tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo da ƙarya da kuma baddala gaskiyar magana dangane da kwangilar aikin wutar lantarki a Mambilla, ta biliyoyin daloli.
Da farko dai an bayar da kwangilar aikin a cikin 2003, ga wani kamfani mai suna Sunrise Power and Transmission Limited. Gwamnatin Obasanjo ce ta bayar da aikin gina tashar samar da wutar lantarkin a wancan lokacin.
A yanzu batun kwangilar ya daɗe ana shari’a tsakanin kamfanin a kotu a wajen ƙasar nan shi da Gwamnatin Tarayya.
A wata tattaunawa da jaridar The Cable kwanan nan, Obasanjo ya ce Agunloye ne ya shirya harƙallar bayar da kwangilar ba tare da amincewar Majalisar Zartaswa ba a lokacin.
To amma a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, Agunloye ya ƙaryata abin da Obasanjo ya bayyana wa duniya dangane da batun kwangilar.
Ya ce ana ƙoƙarin shafa masa baƙin fenti ne, saboda gwamnati na ta borin-kunyar ƙin cika alƙawarin da ta yi a yarjejeniyar kwangilar wutar Mambilla.
Ya ce lallai tabbas gwamnatin Obasanjo ta bayar da kwangilar a cikin 2003, inda kamfanin Sunrise and transmission Limited zai samar da babbar tashar wutar lantarki da babu mai girman ta a ƙasar nan, har migawat 3,050.
To kuma Agunloye ya ce bayan ya sauka daga muƙamin minista a cikin 2003, sai Obasanjo ya canja shawara, ya ce gwamnatin Najeriya ta ce ita za ta riƙa zuba kuɗi ana aikin, maimakon yarjejeniyar farko, wadda ba Gwamnantin Najeriya ce mai zuba kuɗin aiki ba.
Ya ce amma gwamnatin marigayi Umaru ‘Yar’Adua ta soke kwangilar a cikin 2008.
Agunloye ya ce Yar’Adua ya soke kwangilar saboda gwamnatin sa ta gano cewa akwai harƙalla a jami’an gwamnatin Obasanjo, tsakanin 2003 zuwa 2007.
Discussion about this post