Gwamnan Kaduna Uba Sani ya kaddamar da sabbin ƴan banga 7000, da za su rika aikin samar da tsaro a jihar.
Da yake mika su ga rundunar ƴan sanda a Kwalejin horas da Ƴan sanda na Kaduna, ranar Asabar, gwamna Sani ya hori sabbin dakarun, su maida hankali wajen sanin dabarun aiki domin ceto jihar daga masu aikata miyagun aiki.
An zaɓo wadanda aka ɗauka daga duka kananan hukumomin jihar 23. Sannan kuma ya gode wa sarakunan jihar bisa kokarin da suka yi wajen taya gwamnati zaɓo zaƙaƙumen mutanen da za su yi wannan aiki.
Umarnin Uba Sani ga Jami’an tsaro
Gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya umarci jami’an tsaro a jihar su gaggauta gamawa da maharan da suka lashe masallata a ƙauyen Saya-Saya dake karamar hukumar Ikara, jihar Kaduna.
A sanarwar haka da wanda kakakin fadar gwamnatin Kaduna, Mohammed Shehu ya fidda ranar Lahadi, gwamna Uba ya mika ta’aziyyar sa ga iyalan mamatan sannan ya umarci jami’san tsaro su gaggauta kamo waɗanda suka aikata kisan domin a hukunta su kamar yadda shari’a ta gindaya.
Ƴan bindiga sun kashe wasu masallata a lokacin suna sallar Isha a kauyen Saya-saya dake karamar hukumar Ikara Jihar Kaduna.
Ɗan majalisar da ke wakiltar karamar hukumar Ikara a majalisar dokokin jihar Alhassan Muhammed ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa maharan sun far wa wasu ƙauyuka biyu a wannan rana.
“Wannan lamari mai ban tausayi ya faru ne a ranar Juma’a bayan sallar Isha’i, ‘yan bindigar sun mamaye garin Saya-Saya a kan babur da manyan makamai.
“Sun fara harbe-harbe a ciki da wajen masallacin a lokacin sallar isha’i, inda suka kashe mutum bakwai sannan wasu mutum biyu suka ji rauni a wannan masallaci.
“Ina cikin masallacin lokacin da lamarin ya faru, muna sallah, ina cikin harabar masallacin, sai biyu daga cikin maharan sanye da takunkumin fuska, suka tunkari masallacin kafin su fara harbi.
Daya daga cikin maharan daga isowar su ya hura usur, daya kuma ya ce “mun iso” kafin su fara harbin masallatan.
Sun kashe mutane shida a cikin masallacin, kuma na bakwai da aka harba ya mutu a asibitin koyarwa na Aminu Kano, run kafin likitoci su duba shi.
Discussion about this post