Gwamnan Kano, Abba Yusuf ya kori kwamishinan Kasa na jihar Adamu Aliyu, kan kalaman da ya yi na barazana ga Alkalan da ke shari’ar zaɓen gwamnan jihar.
Tun bayan faɗin munanan kalamai da kwamishinan ya yi ga Alkalan da ke shari’ar, da kuma barazanar tada husuma a Kano, husumar da ba a taɓa ganin irin sa ba a Arewa, aka yi ta tofin Allah-tsine ga Aliyu.
PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda Aliyu ya rika tada jijiyoyin wuya a wajen wani taron addu’a inda ya ce Kano ba za ta ga zaman lafiya ba idan har kotu ta yanke hukuncin da ba haka a ba a sharit dake gabanta
Kwamishinan Kasa da Sufiyo na jihar Kano, Adamu Aliyu ya gargaɗi Alkalan da za su yanke shari’ar zaɓen gwamnan Kano cewa duk wanda ya karɓi cin hanci ya juya shari’ar gwamnan Kano, zai ga ‘Bala’i’.
Ya faɗi haka a bidiyo da aka saka a shafukan sada zumunta wanda shi da kansa ya tabbatar da wannan sako da ke cikin bidiyon.
Kwamishina Aliyu ya bayyana cewa akwai raɗeraɗin cewa akwai waɗanda ke yi wa Alkalan tayi cin hanci har naira biliyan 10 domin a kwace gwamnatin Abba a baiwa APC da jam’iyyar ta kada a zaɓen gwamman jihar na 2023.
” Abinda na ke so in gaya wa duk waɗanda ke kokarin yi wa Shari’ar zaɓen gwamna katsalandan cewa ya kwana da shirin ganin bala’in da bai taba ganin irin sa. Ita kanta jihar Kano za ta tarwatse, don ba za mu yarda ayi mana karfakarfa ba.
” Ina gargadin alkalan kotun su sani, duk alkali da ya bari aka yi amfani da shi ya karbi cin hanci ya yanke hukuncin da ba haka ba, muna so mu gaya masa ya zabi tsakanin ransa da kudin cin hancin da ya karba.
” Kuma ina so ku gani kuma ku sani, bala’in kashe-kashen da ƴan Kaduna, Katsinawa da Zamfara suka yi fama da shi, zai zama wasan yara, domin na Kano sai ya dama haka ya shanye, idan aka kwace kujerar gwamnan Kano.
Kwamishina Aliyu ya tabbatar mana da cewa ya faɗi haka kuma bai janye koda harafi daya saga cikin kalaman sa ba.
Har yanzu dai ana jiran kotun sauraron kararrakin zaɓen gwamna, ta yanke Shari’ar Zaɓen gwamnan Kano da na wasu jihohin da ake kalubalantar sakamakon zaɓukan.
Discussion about this post