Ƙungiyar Haɗin Kan Ƙasashen Afrika (AU) ta dakatar da Gabon daga ƙungiyar, kuma ta nemi sojojin da suka kifar da Gwamnatin Ali Bongo su gaggauta bayar da mulki ga farar hula.
Sanarwar da AU ta aiko wa PREMIUM TIMES, ta ce “an dakatar da Gabon daga shiga duk wata hulɗa da AU, har zuwa lokacin da ƙasar ta koma hannun farar hula.”
A ranar Laraba ce da jijjifin safiya sojoji a ƙarƙashin Babban Kwamandan Dakarun Sojojin Shugaban Ƙasa su ka ƙwace mulki daga hannun Ali Bango, wanda ya shafe shekaru 14 ya na mulkin Gabon.
Ali ya hau mulki ne a cikin 1997, bayan rasuwar mahaifin sa Omar Bango, wanda shi kuma ya shafe shekaru 41 ya na mulkin ƙasar Gabon.
An tsige Ali Bongo wanda yanzu haka aka yi masa ɗaurin talala a gidan sa, bayan an gudanar da zaɓen dasojoji aikace akwai maguɗi da murɗiya a zaɓen.
Shugaban Sojojin Mulki, Janar Brice Nguema ake sa ran rantsarwar a ranar Litinin, matsayin shugaban ƙasa na mulkin soja.
“AU na kira sojojin da suka ƙwace mulki a Gaban su gaggauta maida mulki ga zaɓaɓɓar gwamnati cikin gaggawa.”
Juyin mulkin Gabon ya sa an ɗauke hankali daga abin da ke faruwa a Nijar, ƙasar da ECOWAS ta bai wa Sojojin Mulki wa’adin maida hamɓararren Shugaban Ƙasa, Mohammed Bazoum kan mulkin sa.
EU ta ce ta bayar da tazarar kwanaki 15 ga masu ruwa da tsaki cewa a sake zama domin bin ba’asin halin da Gabon ke ciki.
Yayin da al’ummar Gabon ke murnar hamɓarar da Ali Bongo, ƙasashen waje kuwa sai Allah-wadai da juyin mulkin su ke yi.
Discussion about this post