An bayyana cewa fiye da mutum 2,000 suka rayukan su zuwa ranar Lahadi sanadiyyar girgizar ƙasa a Morocco.
An sanar cewa girgizar ƙasar ta kashe mutum 2,122, ta raunata wasu 2,421 a birane shida a ranar Juma’a a ƙasar, kamar yadda Aljazeera ta ruwaito.
Wannan girgizar ƙasar dai ita ce mafi muni da Morocco ta fuskanta a cikin shekaru 60.
Mutane da yawa sun rasa gidajen su da dukiyoyin su sanadiyyar girgizar ƙasar.
Hukumar Binciken Duwatsu da Tsaunuka da Ƙasa ta Amurka, USGS ta ce ƙarfin girgizar ƙasar ya kai ma’aunin 6.8 a Oukaimedene.
Binciken ya ce daga dogayen tsaunukan Morocco da ke nisan kilomita 75 daga Marrakech ne girgizar ƙasar ta fara jijjiga.
Mahukuntan Morocco sun bada hutun kwanaki uku na zaman makoki da alhini da jimami.
Tsohon garin Marrakesh na daga wuraren da girgizar ƙasar ta shafa, wanda birni ne mai tarihi, kuma wanda Hukumar UNESCO ta keɓe a matsayin Cibiyar Bunƙasa Al’adu.
Tuni dai UNESCO ta ce za ta taimaka a sake gina wuraren da girgizar ƙasar ta lalata a birnin.
Kungiyar Red Cross ta Duniya ta ce za a ɗauki shekaru kafin komai ya koma daidai.
Shugabannin duniya, ciki har da Shugaba Bola Tinubu na Najeriya sun aika da saƙon ta’aziyya, tausayawa da alhini ga Morocco.
Discussion about this post