Abin da ya fi ɗaukar hankalin ma’aurata da dangin ango ko na amarya, har ma da sauran abokan ango da na amarya, shi ne saye-sayen kayayyakin shagalin biki. Amma sau da dama ba a damu da bibiyar tarihin salsalar yadda rashin lafiya ke bin jinsi a matsayin gado har ta kai kan wani, ko wata ba.
Soyayya a aure daban, batun cikakkar lafiya kuma ita ma daban.
Ga wasu gwaje-gwaje 10 da likitoci suka bayar da shawara cewa a yi muhimmin la’akari da su.
1. Gwajin Jini (Complete Blood Count):
Akwai buƙatar yin cikakken gwajin jini, domin auna yiwuwar ko akwai wasu ciwuka irin su ciwon suga, hawan jini da sauran su.
Yin haka zai bayar da damar irin shawarwarin da ya kamata a bayar don a kiyaye.
2. Gwajin Ƙwayoyin Halittar Gado (Genetic Testing):
A nan za a yi gwaji domin a gano ko akwai tasirin cututtukan da aka gada tun a kakanni ko kakan-kakanni. Sai kuma gano irin waɗanda ake gudun kada ɗa ko ‘ya’yan da za a haifa su ma su ɗauka ko su kamu da su.
3. Gwajin Cututtuka Jima’i:
Akwai cututtuka da dama da a kan ɗauka daga mace zuwa namiji, ko daga namiji ta hanyar jima’i. A Turance ana kiran su STD, sun kama tun daga ciwon sanyi har zuwa cutar HIV da sauran su.
Yin wannan gwaji ya na da muhimmanci, domin ma’aurata za su san matsayin lafiyar su, ta yadda za su ɗauki matakai daban-daban don kula da kan su.
4. Gwajin Sanin Rukunin Jinin Ma’aurata (Genotype Test):
Ana yin gwajin sanin rukunin jinin ma’aurata domin dalilai da dama, ciki har da sanin yiwuwar ɗaukar ciki lafiya, a yi laulayi lafiya, kuma a haifi yaro lafiya, ya tashi cikin ƙoshi lafiya, ba tare da haihuwar yaro da cutar da ya ɗauka daga jinin uwa ko uba ba.
Haka wannan gwaji na iya gano ko akwai yiwuwar ɗaukar cutar kansa.
5. Gwajin Hawan Jini (Hypertension):
Kuwa da hawan jini a jikin mutum ya na da muhimmanci sosai, domin hakan zai sa a gano sagwangwaman wata cuta ko cututtukan da za a ɗaukar wa matakai tun da wuri.
6. Gwajin Ƙwayoyin Hormone:
A wannan gwaji ana tantance ko rashin daidaiton ƙwayoyin ‘hormone’ zai iya shafar haihuwa ko rashin ta. Wannan gwaji na da muhimmanci ga ma’auratan da suka tsara lokacin fara haihuwa.
7. Gwajin ‘Allergy Testing:
Wannan kuma gwaji ne da ake yi domin a gano yadda mutum ke tsoron wani abin da ba abin tsoro ba ne. Ko kuma yadda jikin sa ba ya son wani abu wanda ba shi da wata illa ga sauran mutane.
8. Gwajin Nauyi Da Na BMI:
Waɗannan gwaje-gwaje za su bayar da haske dangane kula da nauyi, sai kuma bada shawarwarin yadda za a kula da irin abincin da ba shi da illa a jiki, da kuma buƙatar riƙa motsa jiki.
9. Gwajin Ƙwayoyin Halittar Ɗaukar Ciki:
Wannan gwaji na sa likitoci su gano ko namijin ko matar idan akwai wanda ke fama da wata cutar da ka iya kawo masa ko mata cikas wurin ɗaukar ciki.
10. Gwajin Lafiyar Ƙwaƙwalwa:
Ƙungiyar Likitocin Ƙwaƙwalwa (APM) masu aiki a Asibitocin Kula da Masu Taɓin Hankali sun ce aƙalla akwai mutum miliyan sama da 60 masu ciwon taɓuwar ƙwaƙwalwa a Najeriya.
Da yawa akwai mahaukata cikin tufafin alfarma, waɗanda na su ciwon ba ya motsawa, sai idan rana ta ɓaci.
Yin wannan gwaji zai sa a gane takamaimen halin da ƙwaƙwalwar ango da ta amarya suke. Saboda Hausawa ma sun ce, ‘Hankali ke gani, ido gululu ne’.
Discussion about this post