Abubakar Sambo dai wani ɗan canji ne a Abuja, mai shekaru 44 a duniya. Daga cikin kamfanonin canji 5689 da ke da rajista a ƙasar nan, wato BDC ko Bureaux de Change, akwai na Abubakar ciki.
Baya ga harkar canji, Abubakar Sambo na harkokin kasuwanci dai a Abuja, kuma shi ke da wani kamfani na yin ‘yan kwangilolin samar da kayayyaki a ofisoshi, mai suna Ama Business Solution, wanda shi ne tsanin da ‘yan Kwamitin Majalisar Tarayya masu binciken harƙallar ɗaukar ma’aikatan gwamnatin tarayya su da Shugabannin Jami’o’i su ka riƙa buga harƙallar biyan cuwa-cuwar kuɗaɗen toshiyar baki.
Daga cikin kwastomomin Sambo, akwai wata makaranta mai suna Lead British International School (LBIS), wadda aka kafa a cikin Abuja tsawon shekaru 15 kenan.
LBIS na da rassa a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, sai kuma Osogbo, babban birnin jihar Osun.
Binciken PREMIUM TIMES ya nuna Sambo ya daɗe ya na harkokin kasuwanci da LBIS. An shaida ya sha yi masu canjin daloli zuwa Naira, waɗanda idan su ka ba shi daloli, shi kuma sai ya tura masu Naira ta adadin dalolin da aka ba shi.
Ba a dai san inda makarantar ke samun daloli ba, tunda dai da Naira ake biyan kuɗaɗen makaranta.
To idan haka ne, mene ne dangantakar Abubakar Sambo da Lead British International School (LBIS) da kuma kwamitin Majalisar Tarayya mai binciken harƙallar ɗaukar ma’aikata?
Wane ne mai makarantar, kuma ta yaya makarantar ta shiga cikin ƙarambosuwar harƙallar kuɗaɗe?
Labarin da za mu ba ku zai warware maku komai tare da ƙarin hasken yadda kwamitin Majalisa ya riƙa karɓar kuɗaɗe wurin shugabannin hukumomin gwamnati, cibiyoyi, da ma’aikatu, ciki kuwa har da shugabannin jami’o’i, manyan Kwalejojin Fasaha da na Manyan Kwalejojin Ilmi.
*Mun ba ku labarin yadda Shugabannin Jami’o’i suka riƙa tura Naira biyan bi-biyu a wani asusun banki. Su kuma Shugabannin Mayan Kwalejojin Fasaha da na Manyan Kwalejojin Ilmi, sun yi wata dabara, inda su ka riƙa tura Naira miliyan 3 kowanen su a wani asusun banki daban, wanda gano shi abu mai wahala.
Lead British International School: Makaranta Ko Makarkata?:
An kafa LBIS ranar 24 Ga Janairu, 2008. Kashi 75 na hannun jarin LBIS duk na Oluwole Oke ne, Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Obokun/Oriade, daga Jihar Osun. Kuma shi ne ya tashi a gaban majalisa ya bayar da shawarar a kafa kwamitin binciken harƙallar ɗaukar ma’aikata.
Ba ya cikin kwamitin mutum 39 da aka kafa, amma ya cika yin katsalandan sosai a lokutan zaman kwamitin idan an gayyato shugabannin cibiyoyi da hukumomin da ake zargi sun yi harƙalla wajen ɗaukar ma’aikata ba bisa ƙa’ida ba.
Binciken PREMIUM TIMES ya gano cewa bayan Shugabannin Jami’o’i sun amince za su bayar da cin hancin Naira miliyan 2 kowanen su, sun yi tunanin yadda za su bayar da kuɗaɗen da kuma yadda ‘yan majalisa za su karɓa, ba tare da hukumomin daƙile rashawa da kuma ‘yan jarida sun bankaɗo ba.
Sai kwamitin shugabannin jami’o’i a ƙarƙashin Shugaban Jami’ar Benin, Lilian Salami ta sa Shugaban Jami’ar Jos, Tanko Ishaya domin ya tuntuɓi kwamitin Majalisa su tattauna yadda za a tura masu kuɗaɗen.
An zaɓi Farfesa Ishaya ya tuntuɓi kwamitin domin su tsara yadda za a biya kuɗaɗen, saboda Shugaban Kwamitin Bincike Honorabul Yusuf Gagdi, tsohon ɗalibin sa ne, har ma lacca Ishaya ya gayyace shi ya gabatar a Jami’ar Jos a ranar 30 Ga Maris, 2023.
PREMIUM TIMES ta ji cewa Ishaya ya tuntuɓi Honorabul Oke, mai makarantar Lead British International School, shi kuma ya haɗa shi da ma’aikaciyar makarantar, mai suna Stella Adoga.
Ita Stella ce ta tuntuɓi Abubakar Sambo mai Ama Business Solution, ta ce ya bayar da akawun ɗin da za a tuttura masa naira, shi kuma zai cac-canja kuɗin zuwa dala.
Amma dai Stella ba ta shaida wa Sambo su wa da su wa ne za su tura kuɗaɗen ba, kuma ba ta sanar da shi adadin kuɗin da zai ga an tura masa ba. Ta ce ya shirya idan Farfesa Ishaya ya kira shi, sai kawai ya tura masa lambar akawun ɗin, wasu asusun ajiyar kuɗaɗen sa na banki.
Ranar 16 Ga Agusta, Shugaban Jami’ar Jos, Ishaya ya buga wa Abubakar Sambo waya. Ya yi masa tambayoyi dangane da halin da ake ciki wajen canji. Ya ce ya tura masa lambar akawun ɗin da za a tura masa wasu kuɗaɗe.
Asusun Lambar Harƙallar ‘Yan Kwamitin Majalisar Tarayya:
Ɗan canji Abubakar Sambo, ya aika wa Farfesa Ishaya lambar akawun ɗin sa ta 5400495458, Providus Bank.
Shi kuma Ishaya sai ya tura lambar akawun ɗin ga Farfesa Lilian Salami, ta Jami’ar Benin, ita kuma ta tut-tura wa sauran Shugabannin Jami’o’i. Sannan ta ce kowane Shugaban Jami’a ya rubuta sunan Jami’ar sa wurin tura kuɗaɗen.
Kafin PREMIUM ta fallasa labarin, sun tsara cewa Abubakar Sambo zai canja kuɗaɗen zuwa Dala, ya damƙa wa Stella Adoga, ita kuma ta kai wa Honorabul Oke.
Haɗuwar Wakilin PREMIUM TIMES Da Abubakar Sambo:
Bayan shan wahalar neman sa ba a dace ba, daga ƙarshe wakilin mu ya samu haɗuwa da shi a wani gidan cin abinci sananne da ke Wuse, Abuja.
Sambo ya tabbatar da harƙallar da ‘Yan Kwamitin Majalisar Tarayya da Shugabannin Jami’o’i suka tafka, amma ya ce shi dai bai aikata laifin komai ba, canji ne sana’ar sa kuma ya tura akawun kamar yadda aka ce ya tura zai yi masu canji.
Kafin buga labarin, a baya wakilin mu ya tuntuɓi Oke, amma ya ce ƙarya ce, “babu wani ɗan majalisa in dai nagari ne da zai nemi hukumar da ake bincike ta ba shi toshiyar baki, kuma sannan ya fallasa su.”
Da aka ce ai shi da wasu ‘yan uwan sa ‘yan Majalisa ake zargi da aikata harƙallar, dai ya ce, “babu wani mai hankalin da zai iya yi masu wannan zargi, domin ƙarya da ƙage ne.”
Tuni dai ICPC a ranar Juma’a ta bayyana cewa ta fara binciken harƙallar.
Saura jiran sakamakon bincike da kuma hukuncin da zai biyo baya.
Discussion about this post