Wasu mazauna a unguwanni da cikin garin Kano sun koka kan dokar hana zirga-zirga da rundunar ƴan sandan jihar ta saka tun bayan bayyana hukuncin shari’ar zaɓen gwamna da aka yi ranar Laraba.
Wakilin PREMIUM TIMES ya zagaya wasu unguwanni kuma ya zanta da wasu mazauna garin Kano inda suka shaida masa cewa ba su dalilin saka dokar hana zirga-zirga a jihar ba.
” Babu abinda zai faru bayan hukuncin kotu. Mutane ba su ci sun koshi bane za su ta da husuma. Ai sai an ci an koshi ne ake tunanin yin wani abin.
” Mu a nan Kano kasuwanci ne a gaba, idan ka dakatar da harkokin cinikayyar mu na kwana ɗaya, to sai an samu lokaci mai tsawo kafin abubuwa su koma kanar yadda suke a baya.” Innji Shazali Ibrahim
Wasu da sama sun ce, wannan doka ya hana mutane zuwa cikin garin Kano, domin siyan kaya. Akwai mutane da dama da ke zuwa garin Kano a kullum domin siyan kaya.
” Dalilin wannan doka, mutane ba su shigo gari ba. Kafin mu girgije sai an ɗan samu kwanaki tukunna.
Idan ba a manta ba, kotu ta aiyana Nasiru Gawuna a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen gwamnan Kano.
Discussion about this post