Kimanin kashi 90 cikin 100 na Sanatocin Majalisar Dokoki ta 10 na da shari’ar zabe a kotunan kasar.
Sanata mai wakiltar babban birnin tarayya Abuja, Ireti Kingibe, wanda ta bayyana hakan a wani taron manema labarai a Abuja ranar Laraba, ta ce ‘yan majalisar sun fi maida hankaline wajen shari’ar dake gaban su na zaben 2023.
Kingibe ta jam’iyyar Labour Party (LP) ta yi magana kwana guda bayan da kotun ta sake tabbatar da zaben ta a ranar Talata.
Kingibe ta ce ” Ba za a iya gane me muke yi ba yanzu saboda kusan kashi 90 cikin 100 na sanatocin da ke majalisa duk suna da kararraki a kotunan kasar nan. Hankalin su duk ya koma can. Saboda haka dole sai an kammala shari’o’in nan ne za a afar ganin abinda ake so.
Discussion about this post