Hedikwatar tsaron Najeriya ta bayyana cewa dakarun sojin Najeriya sun kashe ‘yan ta’adda 817, sun kama wasu 1,326 sannan sun ceto mutum 721 da aka yi garkuwa da su a cikin watanni uku.
Jami’in yada labarai na rundunar Edward Buba ya sanar da haka da yake ganawa da manema labarai a makon jiya a Abuja.
Buba ya ce dakarun sun kama masu garkuwa da mutane 42, masu hada baki da ‘yan ta’adda 33, barayin shanu 80, ‘yan ta’adda 325, barayin karafan jirgin kasa 27, masu siyar da bindigogi 73 da barayin man fetur 191.
Ya ce akalla ‘yan ta’adda da iyalan su 4,560 ne suka mika wuya a Arewa maso Gabashin kasar nan.
Dakarun sun kama bindigogi 501, dabbobi 3,577, harsasai 3,269 sannan da wasu makaman da maharan ke amfani da su har 674. Sannan kuma an ceto ɗaruruwan mutane da aka yi garkuwa da su.
A yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, Buba ya ce rundunar ‘Operation HADIN KAI’ sun kashe ‘yan ta’add 240, sun kamo wasu 276 sannan sun ceto mutum 147 da aka yi garkuwa da su.
‘Yan ta’adda da iyalen su 4560 sun mika wuya.
Ya ce jami’an tsaro sun kama bindigogi 169, harsasai 1,195, manyan bindigogi kiran AK-47 guda 57, bindiga kirar GPMG guda daya, bindiga kirar HK21 guda biyu, bindiga kirar FN guda daya, bindiga kirar G3 guda daya, karamin bindiga daya, bindigar mafarauta 22, bindiga double barrel daya, bom guda uku da harsasan manyan bindigogi masu yawa.
A Arewa ta Tsakiya Buba ya ce rundunar ‘Operation Safe Haven’ sun kashe ‘yan ta’adda 94, sun kamo wasu guda 477, an ceto mutum 76 da aka yi garkuwa da su, makamai 82 da harsasai 760.
Ya ce rundunar ‘Operation Whirl Stroke’ sun kashe ‘yan ta’adda 83, sun kamo wasu 104, sun ceto mutum 18 da aka yi garkuwa da su, sun kama bindigogi 37, harsasai 68 da wasu makamai 127.
A Arewa maso Yamma Buba ya ce rundunar ‘Operation Hadarin Daji’ sun kashe mahara 248, sun kama 116 sannan sun ceto mutum 359.
Jami’an tsaron sun kama bindigogi 67, harsasai 926 da wasu makamai 160.
A Kudu maso Kudu rundunar ‘Operation Delta Safe’ sun kashe mahara 69, sun kama barayin man fetur 191 sannan sun ceto mutum 12 da aka yi garkuwa da su.
Ya ce dakarun sun Kona jiragen ruwa na katako guda 249, na’uran tatso mai guda 28, manyan jiragen ruwa guda uku da makamai 51.
A Kudu maso Gabas Buba ya ce rundunar ‘Operation UDO KA’ sun kashe ‘yan ta’adda 80, sun kama ‘yan kungiyar Biafra/IPOB 162 sannan sun ceto mutum 109 da aka yi garkuwa da su.
Ya ce dakarun sun kama bindigogi 63, harsasai 320 da wasu makamai 166.
Discussion about this post