Gobara ta tashi a Kotun Ƙoli da ke Abuja da safiyar nan.
Sai dai kuma zuwa lokacin haɗa labarin ba a san musabbabin tashin wutar ba.
Ma’aikata kowa ya tsere, saboda wutar wadda har bayan ƙarfe 9:30 na safe ta na ci, an kasa shawo kan kashe ta.
Ma’aikatan Kashe Gobara sun garzaya su na ta fama da gaganiyar kashe wutar, wadda aka tabbatar ta ci ofisoshin manyan alkalan Kotun Ƙoli uku.
Gobarar ta tashi a lokutan wannan yanayi, wanda shari’ar zaɓen shugaban ƙasa ta koma Kotun Ƙoli, bayan da Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP suka shigar da ƙarar rashin amincewa da hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa ta yanke.
Discussion about this post