Gwamnatin Najeriya ta kafa kwamiti domin dakile yaduwar cutar diphtheria a kasar.
Zuwa yanzu cutar ta yadu zuwa jihohi 14 da suka hada da Lagos, Osun, Nasarawa, Kaduna, Katsina, Yobe, Bauchi, Gombe, Borno, Zamfara, Jigawa, Plateau, Kano da Babban Birnin Tarayya Abuja.
Ministan kiwon lafiya Muhammad Pate ya ce kwamitin za ta jagoranci yakin dakile yaduwar a jihohin da cutar ta bullo.
Ya ce kwamitin za ta hada hannu da gwamnatocin jihohin da cutar ta barke domin daukar matakan da suka dace domin dakile yaduwar cutar.
Pate ya ce shugaban hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko ta kasa NAFDAC Faisal Shuaib da Shugaban hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC Ifedayo Adetifa za su jagoranci kwamitin.
Sauran mambobin kwamitin sun hada da Shugaban fannin kiwon lafiyar jama’a ta ma’aikatar kiwon lafiya Anyaike Chukwuma, wakilin kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO, UNICEF, ma’aikatar, kwamitin sarakunan gargajiya kan inganta cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko NTLC.
Maganin rigakafin Diphtheria
Ministan ya ce UNICEF ta bai wa Najeriya gudunmawar kwalaben maganin rigakafin cutar diphtheria miliyan 1.2 domin dakile yaduwar cutar.
Wakilin UNICEF Rownak Khan ya ce asusun za ta ci gaba da mara wa gwamnati baya domin ganin ta yaki cutar.
Gwamnatin jihar Kano ne za ta karbi magungunan inda daga nan za a raba wa jihohin da cutar ta bullo.
Cutar Diphtheria
Cutar Diphtheria cuta ce da kwayoyin cutar bacteria mai suna ‘Corynebacterium’ ke haddasa wa.
Cutar ya fi kama yara kananan da manyan mutane musamman wadanda ba su yi allurar rigakafin cutar ba.
Yadda ake kamuwa da cutar
Ana iya kamuwa da cutar idan ana yawan zama kusa da masu fama da cutar.
Idan mai dauke da cutar ya Yi tari ko atishawa ba tare da ya rufe bakinsa ba.
Sannan da yawan yin amfani da kayan da masu fama da cutar suka yi amfani da su kamar chokali, Kofi, hakichin da sauran su.
Mutanen da suka fi yawan kamuwa da cutar
Cutar Diphtheria ya fi kama yara da manya musamman wadanda tun farko ba su Yi allurar rigakafin cutar suna yara ba sannan da kin yin allurar rigakafin yayin da suka girman.
Alamun cutar
Akan gane alamun cutar bayan ranar farko zuwa 10 da kamuwa da cutar.
Alamun cutar sun hada da zazzabi, yoyon hanci, ciwon makogwaron, idanun za su Yi jajawur, tari da Kumburin wuya.
Wasu lokuta mai fama da cutar zai Rika ganin wasu farin abubuwa na fitowa da a kusa da makogwaron sa wanda ke hana mutum iya yin numfashi da hadiyan abinci.
Discussion about this post