An shawarci masu buƙatar ɗaukar ‘yar aiki, ‘yar wanke-wanke da sauran masu yin hidimomin cikin gida, to su riƙa yin ƙwaƙƙwaran bincike tukunna.
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Legas, Idowu Owohunwa ne ya yi wannan gargaɗin, bayan gabatar da wasu masu laifukan da aka kama a Legas kwanan nan.
An ruwaito labarin yadda wani ɗan wanke-wanke a gidan wata mata ya kashe ta, kuma ya kashe mahaifiyar ta, sannan ya danƙara masu sata, kuma ya nemi guduwa.
Ɗan wanke-wanken mai suna Joseph Ogbu, an yanke masa hukuncin kisa tun cikin watan Maris, bayan ya kashe uwarɗakin sa mai suna Oreoluwa John mai shekaru 38 a duniya.
Ogbu ya haɗa har da mahaifiyar uwarɗakin ta sa Adejoke mai shekaru 89, duk ya kashe.
Daga nan kuma sai ya gudu da motar ta, samfurin Camry, da talabijin, wayoyin uku, Power Bank da wasu kuɗaɗe masu yawa.
Sai dai kuma ‘yan sun kama shi a lokacin da ya yi ƙoƙarin guduwa.
Ogbu ya tafka wannan ɓarna kwanaki biyu rak da ɗaukar sa aiki a gidan.
Cikin watan Agusta kuma an ‘yan sanda sun kama direban wata Madam, bayan ya saci motar ta, ya je ya sayar da ita.
Shi ma ‘yan sanda sun kamo shi, kuma su ka gano ashe wani ƙasurgumin ɗan fashi da makami ne, domin har bindigar piston aka samu tare da shi.
“Saboda haka a guji yin gaggawar ɗauko hayar wanda zai riƙa yi maka hidima a gida, har sai an yi ƙwaƙƙwaran bincike tukunna, domin gano haƙiƙanin wanda ko wadda za a ɗauka aikin.”
Kuma ya ce a riƙa binciken shin wanda za a ɗauka ɗin nagari ne, ko kuwa ya taɓa tafka ɓarna har aka ɗaure shi a kurkuku?
Discussion about this post