Bankin Unity wanda ke ƙarƙashin kulawa AMCON, ya fitar da rahoton ɗibga asarar Naira biliyan 38.9 a cikin wata shida.
Asarar ta yi tsananin muni, idan aka yi la’akari da cewa asarar Naira biliyan 1.7 kacal bankin ya yi a ahekarar da ta gabata.
Asarar ta faru ne sanadiyyar dakushewar kaifin da Naira ta yi a kasuwar canjin kuɗaɗen waje da kashi 40% bisa 100% a cikin Yuni.
Tsarin ya tallafa wa masu basussuka na kuɗaɗen waje samun riba mai ɗimbin yawa.
Yayin da wannan riba mai tarin yawa ta sa wasu bankuna su ka raba kuɗaɗe masu yawa a tsakanin masu hannayen jari a bankunan na su.
Hukumar AMCON ce dai ke da kashi 34.2 na hannayen jarin Unity Bank.
Har yanzu dai ba a ƙara jin wani ƙarin bayanan dalilin faruwar haka ɗin ba.
Bayanai sun tabbatar da cewa daga cikin kuɗaɗen har da Naira biliyan 8.9 waɗanda ramce ce ne da aka karɓo a bankin African Ezport-Import Bank, bayan da aka canja su zuwa Dalar Amurka.
Kadarar Unity Bank ba ta wuce kashi 35.1 na jidalin yawan tarangahumar kuɗaɗen da ke kan Unity Bank, har Naira biliyan 688.8.
Unity Bank ya ce ya na nan ya na shirin sake farfaɗowa gadan-gadan.
Discussion about this post