Ina mai amfani da wannan damar domin in tunasar da wasu daga cikin alumma abin da suka riga suka sa ni da kuma wadanda basu da masaniya akan harkar amma suna ganin kamar munyi mata shigar shantun kadangare ne!
Dukkanin rukunin mutane guda biyun nan, dodo daya suke yiwa tsafi. ma’ana babu wanda aka haifa da gogewa ko fikira ta musamman wacce ba kowa ne yake da irin wannan baiwar ba.
Bayyananen banbanci tsakanin matasan yan siyasa da manyan yan siyasa a aikace shi ne
Matashin dan siyasa shi ne wanda yake sadaukar da lokaci, tunani, ilimi da dukkanin muhimman abubuwan da suke karkashin kulawar sa, domin samun nasarar wani tsari da ya gamsu dashi kuma yake fatan samun nasara akai ba tare da tunanin samun kudi abin duniya ba, hakazalika a wajen karamin dan siyasa ne ake samun zahiriyar gaskiya, soyayya, rikon amana da jajircewa domin kyakyawar alaka ko fahimtar da take tsakanin sa da dan takara a kowace jam’iyya.
A daya bangaren kuma manyan yan siyasa, sune mutanen da suka ga jiya- suka ga yau. Sunan su ya tambara a harkar siyasa sakamakon daukar lokaci mai tsayi ana damawa dasu a sabgar. Sai dai kash wadannan manyan yan siyasa suna gudanar da mu’ammilar sune a bisa doron jari hujja ko kuma ince fatake ne masu neman abin duniya ido bude, basa iya sadaukar da lokacin su akan dan takara sai an kusa shiga zabe kuma dukkanin motsin su na siyarwa ne!
Mawuyacin abu ne kaga fuskokin manyan yan siyasa a wajen kafa structure ko gina kowace tafiya, kuma tunanin su iri daya ne a kowace kowace jam’iyya suke. Batun gaskiya, rikon amana, jajircewa da sadaukarwa basa tsarin manyan yan siyasar mu domin sun fi ganewa tsari {kudi}.
Fahimtar Yan takara akan manya da matasan yan siyasa ita ce
Kusan kowane dan takarar siyasa yana fifita manyan yan siyasa akan masu tasowa tare da raina kokarin matasan, saboda kawai sunan su bai yi tasiri ko amo a harkar siyasa ba, bugu da kari har kullum yan takara da yan amshin shatan su kokari suke su dunkufar da nasara ko cigaban da matasan yan siyasa suke kawowa. Dalili a nan shi ne basa so matasan yan siyasan su fahimci cewa karan su ya kai tseko ko kuma sun isa a dama dasu a harkar siyasa sakamakon irin gudunmawar da suke bayar wa!
A karahe ina so inyi tambihi akan cewa, ko an yaba kokarin matasan yan siyasa ko ba a yaba ba, hakan bazai hana duniya fahimtar irin cigaba da kokarin da suke yi ba kuma dole suna da rawar takawa a harkar siyasa.
Rattabawa. Umar Aliyu Musa
Discussion about this post