Ci gaba da ƙididdiga da bincike ya tabbatar da zuwa ranar Laraba sama da mutum 6,000 ne ambaliya ta halaka a ƙasar Libya.
Ambaliya da guguwar dai sun faru a biranen Benghazi, Susa, Bayda, Al-Marj da Derna, tsakanin ranakun Lahadi da Litinin.
Ambaliyar ta fi yin munmunar ɓarna a Derna, saboda birnin kewaye ya ke da tsaunuka masu tsawo sosai, har da masu tsayin ƙafa 10.
Sakataren Ma’aikatar Lafiya na Libya, Saadeddin Abdul-Wakil, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Anadolu cewa adadin mutanen 6,000 da aka bayyana cewa sun mutu, zai iya fin haka, domin ba a kammala ƙididdigewa ba.
Waɗanda ambaliya ta halaka sun haura mutum 6,000 a garuruwa biyar.
Ci gaba da ƙididdiga da bincike ya tabbatar da zuwa ranar Laraba sama da mutum 6,000 ne ambaliya ta halaka a ƙasar Libya.
Ambaliya da guguwar dai sun faru a biranen Benghazi, Susa, Bayda, Al-Marj da Derna, tsakanin ranakun Lahadi da Litinin.
Ambaliyar ta fi yin munmunar ɓarna a Derna, saboda birnin kewaye ya ke da tsaunuka masu tsawo sosai, har da masu tsayin ƙafa 10.
Ɗaya ɓangaren gwamnatin Libya ya ce mutum 5,300 ne su ka mutu, kuma aka ƙididdige gawarwakin su a birnin Derma kaɗai.
Hukumar ta ce adadin zai iya fin haka, saboda waɗanda ake gididdgewar duk waɗanda ambaliya ta ture a gefen ruwan Libya ne.
Ƙasashen duniya daban-daban sai agaji iri-iri su ke ci gaba da aikatawa.
Masar ta fara gina matsugunan masu gudun hijira a cikin ƙasar ta, daidai kan iyakar ta da Libya.
Discussion about this post