Shugaba Bola TInubu ya bayyana cewa saboda ɗimbin tattalin arziki da albarkatu da kuma haziƙan jama’a da Najeriya ke da su, bai kamata a ce ta na fama da talauci, matsalar tsaro da koma baya wajen ci gaba.
Ya yi alƙawarin cewa a ƙarƙashin mulkin sa harkoki za su canja sosai, kuma shi ba irin shugaban da zai ƙasa yin abu ya zo ya na bayar da uziri ba ne.
Tinubu ya bayyana haka lokacin da ya ke karɓar baƙuncin tawaga daga Jihar Ribas, a waɗanda suka kai masa ziyara a Fadar Shugaban Ƙasa, a ranar Alhamis.
Tawagar ta mutum 62 dai ta na ƙarashin Gwamna Siminalayi Fubara, kuma ta ƙunshi shugabannin jam’iyyar APC da PDP.
Tsohon Gwamnan Jihar Ribas kuma Ministan Babban Birnin Tarayya, FCT Abuja da kuma tsohon Shugaban Ƙungiyar Lauyoyi ta Ƙasa, Onieze Okocha su na cikin tawagar.
“Bai dace a ce talauci ya durfafi Najeriya ba. Za mu maida wahala ta koma daɗi. Saboda duk tsananin zafi to akwai sauƙi.
“Mu dai ba ragwaye ba ne. Allah ya albarkaci ƙasar mu. Kawai mu haɗa kai, mu zama ‘yan uwan zuma, kuma mu ƙara kyautata maƙautar mu.
“Ni ba shugaban da zai kasa yin wani abu ba ne ya dawo daga baya ya na bayar da uziri. Zan yi aiki tuƙuru domin ƙasar mu, tare da maida himma ga kishin samar da yalwa da ɗimbin arziki a cikin ƙasa. Amma babu dalilin da talauci zai addabi Najeriya.” Inji TInubu.
Tun da farko, Gwamna Fubara ya shaida wa Tinubu cewa sun kai ziyarar ce domin godewa Shugaba Tinubu, dangane da naɗa Wike muƙamin Minista.
Discussion about this post