Ɗan takarar gwamnan Kaduna na PDP a zaɓen 18 ga Maris, Isah Ashiru ya tabbatar wa mutanen Kaduna cewa shi da jam’iyyar sa ta PDP, Za su bi duk hanyoyin da doka ta tanada domin kwato musu abinda suka zaɓa.
Da ya ke tattaunawa da Talbijin ɗin Channels bayan yanke hukuncin Shari’ar zaɓen gwamna wanda aka yi a Kaduna ranar Alhamis, Honarabul Ashiru ya ce tuni lauyoyin sa da na jam’iyya sun shirya garzaya wa kotun ɗaukaka kara domin a kwato masa nasarar da ya samu a zaɓen.
Ashiru ya ce ” Kotu ba ta ce Uba Sani ne ya yi nasara a zaɓen Kaduna, abinda ta ce a sake zaɓe a wasu mazabu da aka lalata kuri’un su. Wannan shina abinda kotu ta ce. Amma nasara a zaɓe nine na yi, kuma ƴar fara za ta nuna a kotun ɗaukaka ƙara.
” Amma da ya ke su kan su a ruɗe suke sai suka yi gaggawar zuwa jaridu suka rika faɗan abinda ba haka.
Ashiru ya kara da cewa shi fa ba ma kammala zaɓe ya ke magana ba, abinda ya ke jayayya a kai shine a tabbatar da shi zaɓaɓɓen gwamnan Kaduna, domin shine ya yi nasara a zaɓen 2023.
” Abinda muke nema shine a tabbatar mini da kujerar gwamna da na yi nasara a zaɓe. Kowa ya sani mutane Kaduna sun zaɓe ni Isah Ashiru, amma a ka yi mana murɗiya.
” Za mu kotu mu ɗaukaka kara kuma InshaAllahu, muna sa ran za mu yi nasara a kotun ɗaukaka kara ba ma sai mun kai ga zuwa kotun Koli ba. Sai dai idan sune ba su yarda ba su je amma mu za mu karɓe ta tuna kotun ɗaukaka kara
A karshe ya yi kira ga mutanen Kaduna sa magoya bayan sa cewa kowa ya kwantar da hankalin sa a zauna lafiya da juna.
Discussion about this post