Tsohon ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola (SAN), ya ce ba ya bukatar wani mukami da zai yi aiki a gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu, wanda a ganinsa ke haifar da shugabanni masu zuwa nan gaba.
Fashola, na hannun damar shugaba Tinubu ne, ya bayyana haka a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a jami’ar jihar Legas, Ojo, ranar Talata.
Fashola, wanda tsohon gwamnan shugaban fadar gwamnati ne a lokacin da Tinubu ke gwamnan Legas na amsa tambaya da ka yi masa kan gudunmawar da yake bada wa a gwamnatin shugaba Tinubu.
“Bana bukatar mukami don yin aiki, shugaban kasa zai iya nada akalla minista daya ne kawai misali daga kowace jiha.
“Akwai isassun wurare wato ma’aikatu da ba a naɗa shugabannin su ba, sannan kuma ma ƴan Najeriya mutum sama da miliyan 200 ba za a iya naɗa duka ba.
“Dole ne dukkanmu mu taka rawa a matsayinmu na ’yan kasa, kuma dan kasa baya bukatar mukami don yi wa ƙasar sa aiki.
Fashola ya ce dole sai wasu sun matsa kafin na kasa su samu shiga. Zai bada gudunmawar sa ta kowacce hanya don samun nasarar wannan gwamnati ba sai lallai annnaɗa shi wani abu ba.
Discussion about this post