Shiyar Dan majalisa mai wakilta Hadejia a majalisar dattawa ta kasa yayi nasarar samun wakilai wadanda suka shude suka samu yabo daidai misali .
Cikin aiyukan da irin wadannan wakilan suka aiwatar sun hada da samar da Asibitoci , Ruwan sha,inganta harkokin Noma ,Wutar lantarki da sauran su .
Idan muka duba daga kan Sanata Abdul’azeez Turabu yayi namijin kokari wajen samar da Asibitoci, Ruwan sha da wutar lantarki a shiyar Jigawa ta Arewa maso gabas .
Haka idan muka yi dubi zamu ga yadda Sanata Muhammad Ubali Shitu yayi kokari wajen raya harkokin more rayuwa wajen Samar da su a kauyuka, birane da sauran su.
Kasancewar sa ɗan siyasa da ya daɗe yana gwagwarmaya ya yi fice wajen aiyukan raya kasa a kauyukan jihar.
Haka zalika wanda ya maye gurbin sa Sanata Ibrahim Hadejia ya yi kokari irin nasa wajen aiyukan alkhairi da kuma nuna bajinta wajen fito da jihar jigawa a majalisar tarayya wajen bada gudunmawa Ilmance a zauren majalisa tarayya tare da samar wa Matasa aiyukan yi kusan sama da Matasa 110 domin su ma su dogara da kan su.
Kasancewar sa mai hakuri,ilmin zamani ya yi amfani da hakan wajen ilmantar da mabiyansa wajen yin hakuri tare da nuna musu hanya wanda ya dace.
A karshen rubutuna ina yiwa Wanda ya gaje shi Sanata Ambassador Ahmed Abdulhamid Malam Madori fatan alkhairi da kuma fatan fitar da yankin mu kunya kamar yadda magabatan sa suka yi lokacin suna wakiltar yankin .
Alhaji Musa Muhammad Hadejia.
Discussion about this post