Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya yi wa tsohon Mataimakin Kasa Atiku Abubakar wasan Kanuri da Fulani, bayan kammala shari’ar zaɓen shugaban ƙasa, a ranar Laraba a Abuja.
Da ya ke ganawa da manema labarai, Shettima wanda ya shafe sa’o’i 13 ya na kotun, har aka kammala yanke hukunci, ya bayyana cewa Atiku ɗan uwan sa ne, kuma abokin wasan su na Kanuri da Fulani.
“Kowa ya san akwai wasan barkwanci da zolaya na al’ada tsakanin mu Kanuri da kuma su Atiku Fulani.
“Saboda haka ina da damar da zan zolaye shi yadda na ke so, kuma babu abin da zai yi min.
“To mu ba ritaya za mu yi wa Atiku ya koma Dubai ko Morocco da zama ba. Ritaya za mu yi masa ya koma Fombina, ni kuma zan sai masa awaki da kajin da zai yi rayuwar sa a can ya na kiwo.”
Haka Shettima ya bayyana cikin barkwanci da zolaya kan rashin nasarar da Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa ta bai wa Atiku.
Sai dai kuma bayan ya gama zolayar Atiku, Shettima ya bayyana cewa, Atiku mutum ne nagari wanda a gaskiya Najeriya na buƙatar sa domin ciyar da ƙasa gaba.
“To maganar gaskiya a ajiye zolaya da barkwanci a gefe. Atiku haziƙin mutum ne, nagari, wanda a yanzu ko a kasuwa samun kamar sa zai yi wahala. Najeriya na buƙatar Atiku domin haɗa kai a ciyar da ƙasa gaba. Yanzu batun mulki ake yi, ba batun siyasa ba.”
PREMIUM TIMES Hausa ta kalli faifan bidiyon da Shettima ya yi wannan bayani, wanda gidan talbijin ya ɗauka.
Discussion about this post