‘Yan takarar zaɓen shugaban ƙasa na 2023, Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na APC, sun bayyana cewa Alƙalan Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓen Ƙasa ba ta yi wa hujjojin da su ka gabatar filla-filla ta tsetstsefe su ba.
Sun bayyana na Kotun Ƙoli cewa Kotun Ɗaukaka Ƙarar sama-sama ta bibiyi hujjojin na su, shi ya sa ta ba su rashin nasara.
Cikin ƙararrakin da suka shigar daban-daban, Atiku da Obi sun bayyana cewa rashin aika sakamakon zaɓe daga BVAS a zamanance kamar yadda INEC ta ce za ta yi, kuma kowa ya sakankance cewa za a yi hakan, su ka ce babban dalili ne na soke zaɓen.
Sun kuma ce haka shi ma rashin samun kashi 25% bisa 100% na ƙuri’un FCT Abuja da Bola Tinubu ɗan takarar APC bai yi ba, shi ma hakan ya nuna cewa bai cancanta a bayyana cewa shi ne ya yi nasara ba.
Sun ce doka cewa ta yi, “tilas wanda ya yi nasara ya kasance ya samu aƙalla kashi 25% bisa 100% a jihohi 2 bisa 3 na yawan jihohin Najeriya 36, DA Abuja.”
A kan haka su ka ce tunda doka cewa ta yi ‘DA’ Abuja, kwanan Abuja ba ta cikin adadin jihohi 36 na Najeriya. Kuma dama ai ko makaho da mahaukaci sun san FCT Abuja ba jiha ba ce.
Sun ce INEC tun farko ta shirya maguɗi a zaɓen, domin a lokaci ɗaya aka yi zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisar tarayya da Sanatoci.
“Me ya sa a zaɓen sanatoci BVAS bai samu matsalar aika sakamakon zaɓe ba, sai a zaɓen shugaban ƙasa?” Inji bayanan su.
Atiku dai ya dira Kotun Ƙoli da lauyoyi 67, waɗanda 18 daga cikin su duk Manyan Lauyoyi ne, wato SAN.
Sun ce duk mai tantamar Abuja ba jiha ba ce idan ana maganar samu ko rashin samun kashi 25% bisa 100% na ƙuri’un FCT Abuja, to ya duba Dokar Zaɓen Najeriya, Sashe na 13 (2) (b).
Sun kuma ce a duba Sashe na 64(4) a ga abin da doka ta ce dangane da BVAS.
Discussion about this post