Kotun sauraron kararrakin zaɓen gwamnan jihar Kaduna na yanke hukunci karar da PDP ta shigar tana ƙalubalantar nasara Uba Sani ta manhajar Zoom.
An tsaurara matakan tsaro a harabar kotun domin gudun tashin hankali bayan sanar da hukuncin kotun.
Ɗan takarar gwamnan jihar a jam’iyyar PDP, Isa Ashiru ne ke ƙalubalantar nasarar gwamna Uba Sani na jam’iyyar APC in da ya ce ba shi ne ya yi nasara a zaɓen gwamnan ba.
Discussion about this post