Lokacin da aka ƙara kuɗin manyan makarantun Kaduna, lokacin mulkin gwamna Nasir El-Rufai, mutanen Kaduna sun hayayyaƙo domin nuna rashin amincewar su da wannan kari da El-Rufai ya yi. Sai dai kuma a lokacin gwamnatin jihar ta rika nuna wa iyayen yara cewa ba za ta janye ba ko ta yi ragi da wannan kuɗaɗe da ta kara na manyan makarantu.
A wancan lokacin makarraban gwamnati, da suka hada da mataimakiyar gwamna, Sakataren gwamnatin jihar da shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar Mohammed Abdullahi, sun bi ɗaliban har makarantun su suna nuna musu cewa dole iyaye su hakura da ƙarin, abin ya fi ƙarfin gwamnati, ba za a rage karin ba.
Dalilin wannan kari na kudin makaranta, wasu da ba za su iya biya ba suka cire ƴaƴan su, wasu kuma suka tsunduma cikin cin bashi domin biya wa ƴaƴan su kudin karatu.
El-Rufai ya nuna wa ƴan Kaduna cewa ya zama dole a yi wannan kari, saboda jihar na bukatar kudin gina gari.
Sai dai kuma tun bayan canja gwamnati da aka yi, aminin sa, Uba Sani ya gaje shi, sai aka fara samun sauye sauyen da muke ganin da El-Rufai ne ke mulki da ba haka ba. Wannan sauye sauye sun hada da rage kudin makaranta da gwamnatin baya ta kara.
Abinda gwamnatin Uba Sani ta yi nuni ne cewa abin dai tun farko rashin tausayi ne, ashe za a iya rage karin ta yadda talakawa za su iya biya, suma ƴaƴan su su iya karatu a manyan makarantun jihar. Gwamna Uba Sani ya na da tausayin talakawa kuma ya na sara ya na duban bakin gatari.
Ko da ya ke wasu na ganin ya watsa wa El-Rufai kasa ne a ido tashin farko ya nuna matakan sa da wasu daga cikin ayyukan da ya yi ba don kishin talaka a ka yi su ba, an yi su ne don son rai. Ko da yake yanzu aka fara tafiya, kwanakin su 100 kenan a kan mulki, ba za a iya cewa ga takamaiman inda akalar gwamnatin ta sa ta fuskanta ba, kila bayan yanke hukuncin Shari’a da ake yi wanda PDP ke ƙalubalantar nasarar APC a kotu za a tabbatar da inda aka dosa a gwamnatin idan ta yi nasara a Kotu.
Wani abu da tashin farko ya bambamta da gwamnatin El-Rufai shine, Uba Sani ya tara ƴan siyasa ne ba ma’aikata ba, sannan akwai bambamci wajen irin ma’ikata, musamman kwamishinoni da masu taimaka masa da ya ɗiba. El-Rufai ɗan Boko ne, kuma ɗan siyasa, ya na son kwarewa ba surutu ba. Shi ko Uba a nawa hasashen, ya fi gane wa na kusa da shi a siyasan ce, da ƴan cika baki fiye da kwarewa da jajircewa.
Aisha Imran Alhaji, marubuciya daga Kaduna
Discussion about this post