Kodinetan Cibiyar Binciken da Daƙile Ta’addanci da ke ƙarƙashin Ofishin Mashawarcin kan Harkokin Tsaro, Yaminu Musa, ya bayyana cewa ana amfani da kuɗaɗen fansar da ‘yan bindiga masu garkuwa ke karɓa wajen ɗaukar nauyin ta’addanci.
Musa wanda tsohon Sojan Ruwa ne, ya bayyana haka a wajen wani tattauna hanyoyin daƙile garkuwa da mutane, wanda aka Ofishin Mashawarci kan Harkokin Tsaro ya shirya taron.
Ofishin na ONSA ya shirya taron ne da haɗin guiwa da Ofishin Jakadancin Birtaniya da ke Abuja, Najeriya’.
“An gano cewa ana karkatar da miliyoyin kuɗaɗen fansar da masu garkuwa ke karɓa, wajen ɗaukar nauyin ta’addanci a Najeriya.
Ya ce muhimmancin haɗa kai tsananin kafefen jaridu domin a kakkaɓe ta’addanci a ƙasar nan.
“A halin yanzu da duniya ta ke dunƙule wuri ɗaya a soshiyal midiya, inda bayanai ke saurin taɗuwa a ɓangarorin sadarwa, to fa kafafen yaɗa labarai su da haƙƙin rage kaifin labarai masu nasaba da matsalar tsaro.
“Sakamakon abin da ke faruwa bayan an watsa wa duniya labarai na bogi, lamarin kan yi wa ƙoƙarin daƙile ta’addaci babbar illa.” Inji shi.
Discussion about this post