Tabbatattun bayanai sun nuna yadda ‘yan bindigar da suka kutsa gidajen kwanan ɗaliban Jami’ar Gusau suka kwashi mata, suka nausa da su cikin Dajin Kuyambana.
‘Yan ta’addar sun afka gidajen kwanan ɗalibai mata har uku a Sabon Gida, kusa da Gusau, babban birnin Jihar Zamfara, suka jidi mata 24 kan babura, a ranar Juma’a.
Zuwa ranar Talata dai gamayyar zaratan jami’an sojoji, ‘yan sanda da sauran jami’ai sun ceto 13 a arangama biyu da suka yi.
Mazauna yankin Sabon Gida ciki har da basaraken gargajiyar yankin, waɗanda suka ga yadda lamarin ya faru, sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa bayan ‘yan bindiga sun kai farmakin, sun riƙa kwasar matan su na darzazawa dajin Ɗansadau a cikin Ƙaramar Hukumar Maru, a tsakanin ranakun Juma’a da Litinin.
Sun riƙa yin walankeluwa da matan kan babura a yankin Dajin Kuyambana.
Wannan jarida ta gano cewa ‘yan bindiga da matan da suka kwashe sun kwana a cikin masallaci a ranakun Asabar da Lahadi, a wasu ƙauyuka biyu na yankin Ɗansadau.
Mazauna yankin sun tabbatar da cewa ranar Litinin kuma ‘yan bindiga tare da matan da suka kwashe sun isa Dajin Madada, daji mafi wawakeken faɗi a Gandun Dajin Kuyambana.
Dajin Kuyambana: Gandun Dajin Gwamna A Hannun ‘Yan Bindiga:
An tabbatar da Dajin Kuyambana a ƙarƙashin ikon ‘yan bindiga ya ke, waɗanda ke ƙarƙashin gogarma Ali Kachalla da Dogo Giɗe. An kuma haƙƙaƙe cewa Ali Kachalla da Dogo Giɗe ne suka tura aka kwaso matan da ƙarfin muggan makamai.
‘Yan Bindiga Sun Yada Zango, Suka Kwana Cikin Masallaci:
“Bayan sun kwashi matan daga gidajen kwanan ɗaliban jami’a uku, sun zarce Gajeren Ƙauye da ke kilomita uku kusa da Ɗansadau. A Gajeren Ƙauye suka gwamutsu a cikin masallaci ɗaya suka kwana. Ranar Lahadi kuma suka nausa ƙauyen Kukar Magu da ke tazarar kilomita takwas daga garin Ɗansadau.
Sun isa sansanin su cikin Dajin Madada safiyar Litinin, inda suka jera wa gogarman su Ali Kachalla matan da suka kamo daga Jami’ar Gusau.”
Wani mazaunin yankin da ya roƙi mu ɓoye sunan sa ne ya tabbatar da haka ga PREMIUM TIMES.
Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Jihar Zamfara, Yazeed Abubakar ya ce ‘yan sanda ne ya kamata a sanar wa da irin wannan labari da wuri-wuri, domin su kai ɗaukin ceto.
Ya ce jami’an tsaro na kan ƙoƙarin cewa waɗanda ke hannun ‘yan bindiga ɗin.
“Muna roƙon jama’a su riƙa bai wa jami’an tsaro irin waɗannan bayanai cikin hanzari, domin su kai ɗauki da gaggawa.” Inji Kakakin ‘Yan Sandan Zamfara.
Yadda Kachalla Da Dogo Giɗe Suka Kafa Ƙaƙƙarfar Dabar Tara Kuɗaɗen Fansa:
An haƙƙaƙe cewa Ali Kachalla da Dogo Giɗe sun fi sauran ‘yan bindiga kafa ƙaƙƙarfar dabar tara kuɗaɗen fansa a Arewa maso Gabas da Arewa ta Tsakiya.
A na su tsarin garkuwa da mutane, sun haramta wa yaran su kai farmaki cikin ƙauyukan kewayen Dajin Kuyambana. Sun fi maida hankali wajen kai hare-hare a makarantun gwamnati, kama jami’an gwamnati, ko hari a cibiyoyin gwamnati. Sukan tare matafiya su yi garkuwa da su, musamman waɗanda ke cikin motocin gwamnati.
Irin wannan salon garkuwa da su ke yi, sai su kuma mazauna ƙauyukan da ke kusa da dajin ke jin daɗin maƙauyaka da irin su Kachalla da Dogo Giɗe, saboda ba su kai masu hare-hare, kuma babu wasu masu garkuwar da za su iya tsallakawa daga wasu dazuka su kai masu hari.
Mazauna yankunan karkara da dama sun ce an samu sauƙin kai hare-hare ne a yankin Ɗansadau sakamakon umarnin da su Dogo Giɗe suka yi cewa a daina kai wa ƙauyuka farmaki.
Sun daina kai hare-hare, sai dai su kan tura ‘jakadun su’ cikin Ɗansadau domin a yi sulhun sasanta rikici. Idan kuma wasu ‘yan bindiga su ka yi gangancin kai wa mazauna yankin hari, to su Dogo Giɗe kan sa a ladabtar da su.
Kada a manta, su Dogo Giɗe ne suka kwashi ‘yara ‘yan makaranta 136 daga Islamiyyar Salihu Tanko a garin Tegina, cikin Ƙaramar Hukumar Rafi, a Jihar Neja, a ranar 39 ga Mayu, 2021.
Su ne kuma su ka jidi ɗalibai da malaman Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Yawuri, a Jihar Kebbi, cikin watan Yuni, 2021.
Su ne kuma a baya su ka riƙa kai wa makarantun sakandare hare-hare a Katsina da Kaduna, har sai da ta kai aka rufe dukkan makarantun da ake tsoron za a iya kai wa farmaki.
Majiya ta ce dabar Kachalla da ta Dogo Giɗe kan karkasa waɗanda suka kama a tsakanin su, daga nan sai su riƙa yin jinga da gwamnati ko iyayen waɗanda suka kama, su yanka farashi, ana tayawa, su na cewa albarka.
Dajin Kuyambana da ke cikin Ƙaramar Hukumar Ɗansadau, ya mamaye murabba’in sikwaya kilomita 492 a Jihar Zamfara. Yanki ne mai albarkar noma da kiwo.
A baya PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin yadda ‘yan bindiga suka ragargaji Sansanin Zaratan Sojoji a ƙauyen Matunji da ke ƙarƙashin yankin Ɗansadau. A farmakin sai da suka kashe Sojojin Sama 9, ‘yan sanda 2, da soja 1.
A dajin Ɗansadau, ‘yan bindiga na mamaye ƙauyukan da dabu jami’an tsaro, su tsige dagaci ko mai unguwa, su ƙaƙaba wa jama’a harajin ladar kula da tsaron su. Wanda ba ya iya tsayawa kuwa, su ce ya bar garin, ya ƙara gaba.
Discussion about this post