Dan takarar gwamnan Kaduna na jam’iyyar PDP ya bayyana rashin amincewar sa da hukuncin kotun sauraren karar zaben gwamnan Kaduna wacce ta yanke hukunci ranar Alhamis a Kaduna.
Ashiru ya ce kotu ba ta bi ba’asin abin da PDP da shi kansa suka mika gabanta ba a dalilin haka ya sa ba za su hakura ba za su garzaya kotun daukaka kara domin bibiyar nasarar jam;iyyar a zaben Maris.
Idan ba a manta ba Kotu a Kaduna ranar Alhamis ta yanke hukuncin yin watsi da karar da Ashiru ya shigar na kalubalantar nasarar da hukumar zabe ta aiyana cewa wai Uba Sani na APC ne ya yi nasara a zaben gwamnan jihar.
Kotun ta ce wai dalilin da ya sa bata bata loacinta wajen bin ba’asin korafe-korafen PDP da ta mika gabanta ba shine don ta tun farko jam’iyyar ta karya dokar kotu.
Dokar kuwa ita ce wai bata shigar da wasu takardun kara ba a lokacin da yakamata sai sai da wa’adin haka ya wuci kamar yadda doka ta gindaya.
Sai dai kuma a sakon Ashiru ga magoya bayan sa da na PDP ya ce tabbas za su garzaya kotun daukaka kara domin ci gaba da shari’ar kwato wa mutanen Kaduna abinda suka zaba.
” “Kotu ta rabu kashi 2:1 a kan haka, ta soke zaben gwamnan jihar Kaduna, ta kuma ba da umarnin a karbo takardar shaidar cin zabe tare da gudanar da sabon zabe a wasu rumfunan zabe a kananan hukumomi 4 sannan a yi la’akari da sakamakon da ya biyo baya. kafin a bayyana wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kaduna.”
Discussion about this post