Mai Shari’a ya bada umarnin a buɗe asusun akawun ɗin makusancin Shugaba Bola Tinubu, Mudashiru Obasa, wanda aka kulle tun cikin 2020.
Wannan al’amari dai ya faru ne a Babbar Tarayya da ke Legas, inda ake shari’ar kulle asusun ajiyar kuɗaɗen Kakakin Majalisar Jihar Legas, Mudashiru Obasa.
Tun da farko dai EFCC ce ta nemi kotu ta ba ta iznin kulle asusun ba ɗaya ba, domin ta binciki wata harƙalla.
A wancan lokacin, EFCC ta ce ta nemi kulle asusun domin ta binciki harƙalla, haɗa baki ya karkatar da kuɗaɗe, cin amanar aikin ofis da sauran laifukan zamba.
Takardun kotun da PREMIUM TIMES ta ci karo da su, sun tabbata hujja cewa Mai Shari’a Nicolas Oweibo ya bayar da umarnin a buɗe asusun ajiyar kuɗaɗen dukkan su tun a ranar 16 Ga Agusta, bayan da lauyoyin sa su ka rubuta takardar neman a biya masu wannan buƙata.
Asusun akawun-akawun ɗin dai guda uku ne, waɗanda ke maƙare da na’urori da Daloli a Standard Chartered.
An buɗe asusun duka uku a gaban lauyan EFCC, a kotu, amma an keɓe ba a gaban jama’a ba. Kuma lauyan EFCC bai yi wata jayayya ba.
Discussion about this post