Ambaliyar ruwan saman da aka yi a kauyen Dakingari dake karamar hukumar Suru jihar Kebbi ya yi ajalin mutum uku.
Ambaliyar ya faru ne bayan ruwan saman da aka yi kamar da bakin kwarya a ranar Asabar din da ya gabata.
Shugaban karamar hukumar Muhammad Suru ya ce ambaliyar ya yi sanadiyyar asarar dukiyoyin mutane na miliyoyin kudade.
“ Garin Dakingari ya yi shekara sama da 20 yana fama da ambaliyar ruwa duk da cewa gwamnatocin Nasamu Dakingari da Atiku Bagudu sun yi kokari sun gina hanyoyin ruwa amma duk shekara sai mun samu ambaliyar ruwa.
Ya ce za a iya maganin ibtila’in ambaliyar ruwan ne idan aka katange kauyen sannan da fitar da hanyoyin ruwa a tsaunikan dake kusa da kauyen.
Suru ya yi kira ga mazauna kauyen da su guji gina gidajen su a kan hanyar ruwa, su guji toshe hanyoyin ruwa da zubar da bola yadda ya kamata domin guje wa akuwar ambaliyar ruwa.
Discussion about this post