Aƙalla an tabbatar da mutuwar mutum 3,000, sannan ana cigiyar sama da mutum 10,000, bayan mahaukaciyar guguwa ta yi sanadiyyar ɓallewar dam biyu, har ambaliya ta halaka dubban mutane a Libya.
Mummunan lamarin ya faru a birnin Derna da wasu garuruwan Arewa maso Gabacin Libya.
“An samu asarar rayuka da dama, kuma wajen 10,000 sun ɓace ba a ji ɗuriyar su ba.”
Haka Jagoran Red Cross na Ƙasa-da-ƙasa, Tamer Ramadan ya bayyana a ranar Talata.
Ministan Harkokin Lafiya na Libya, Othman Abduljalil, ya shaida wa Gidan Talbijin na Almasar da ke Libya cewa, aƙalla an nemi mutum 6,000 a birnin Derman, an rasa su.
Ya ce a yanzu birnin Derman ya zama kufai, gawarwaki ke birjik ko’ina, waɗanda su ka tsira da ran su kuwa su ma a cikin mawuyacin halin da ba su iya gaba, ba su iya baya su ke.
Jami’in Tattalin Arziki da Walwala mai suna Mahmoud Iftessi, ya shaida wa Aljazeera cewa rashin kula da madatsun ruwan biyu ne ya haddasa ɓallewar su a lokacin ruguwar.
“Dam ne guda biyu su ka ɓalle, su kuma mutane su na ta gina gidaje a kan gefen kogi. Wannan shi ne ya haifar da matsalar.”
“Wannan lamari ya ma fi ƙarfin mu kira shi balbalin bala’i. Idan akwai wata kalmar da za mu kira shi, wadda ta fi balbalin bala’i, za mu kira abin a hakan.”
Aljazeera ta ce masu ceto ba su iya isa birnin Derna, saboda ruwa ya shafe ko’ina.
Tuni wasu yankunan da za a iya kai ɗauki su ka samu isar masu agajin gaggawa da jami’an tsaro.
Shugaban Masar, Abdel Fattah el-Sisi, ya umarci sojojin ƙasar su hanzarta kai ɗauki Libya.
Jiragen helikwafta masu ceto da kai agaji daga Turkiyya sun isa Libya har sun fara aiki.
Discussion about this post