Ministan Babban Birnin Tarayya, FCT Abuja, Nysome Wike, ya nuna rashin amincewa dangane da yadda aka ƙulla wata yarjejeniyar kwangilar gina gidaje masu sauƙin kuɗi har na Naira biliyan a yankin Wasa, da ke Gundumar Wasa.
Wike ya nuna ɓacin rai dangane da yadda aka rattaba yarjejeniyar, wadda ya ce an yi wa Hukumar FCT Abuja sagegeduwa da saki-na-dafe a kwangilar.
A ranar Litinin ce Minista Wike tare da Ƙaramar Ministar Abuja, Mariya Mahmoud da wasu jami’an gwamnati su ka ziyarci inda ake aikin titin wurin da aka fara aikin gina gidajen, a Wasa da ke can gaba da Kabusa.
Tun da farko dai babban jami’in kula da Ayyukan Bunƙasa Yankunan Gefen Babban Birnin Tarayya, Olusegun Olusan, ya bayyana wa Wike cewa an bayar da kwangilar tun cikin 2014 a kan kuɗi Naira biliyan 26. Amma cikin 2018 bayan shekara huɗu, sai aka maida kwangilar zuwa Naira biliyan 85.
Olusan ya ci gaba da shaida wa Wike cewa zuwa yanzu dai an biya kamfanin da ke gina gidajen Naira biliyan 21, ba a cika masa Naira biliyan 64 ba.
“Sannan kuma zuwa yanzu dai aikin da aka fara ya kai kashi 22.4, saura kashi 77.6 ke ba a kammala ba.” Cewar Olusan.
Sagegeduwa A Kwangilar Naira Biliyan 85:
Olusan ya shaida wa Minista Wike da Mariya Mahmoud cewa a yarjejeniyar kwangilar, gwamnatin FCT Abuja za ta bayar da fafareren filin da za a gina gidajen, sannan kuma ta yi titina zuwa unguwar da cikin layukan da ke unguwar da aka gina gidajen. Shi kuma kamfanin gina gidaje mai zaman kan sa, zai gina gidaje ya sayar ga marasa galihu a kan farashi mai rahusa.
“An tsara cewa za a gina ƙananan gidaje masu ɗakuna bi-biyu, a sayar a kan Naira miliyan 7 ga marasa galihu.” Inji Olusan.
Ya na zuwa daidai nan, sai Wike ya yi caraf ya ce “wannan ai sagegeduwa ce. Gwamnati ba za ta kashe Naira biliyan 85 ta gina titina ba, sannan ta bayar da fili kyauta ga kamfanin gina rukunin gidaje, shi kuma ya gina gidaje ya sayar, gwamnati kuwa ba a amfani ko sisi ba kenan.”
“Gaskiya ba mu gamsu da wannan tsarin ba, wanda Gwamnatin FCT ta yi a baya. Babu yadda za a yi fa gwamnati ta amayar da Naira biliyan 85 haka kawai kuma ta bayar da fili, wani ya gina gidaje ya sayar. Wace irin sagegeduwa ce wannan.
“Irin wannan sagegeduwa ba abin amincewa ba ce kwata-kwata. Tunda gwamnati ce ta bayar da fili, kuma ita za ta gina titina da kayan more rayuwa a rukunin gidajen, to tilas ita ma sai an yi komai tare da ita.”
Wike ya ce a irin wannan tsari ai gwamnati da kan ta ke yanka wa gidajen farashin yadda talakawa za su iya saye.
Ya ƙara da cewa shi dai bai ga yadda talaka zai iya sayen gidan Naira biliyan 7 ba.
Daga nan ya ce shi dai ba zai ƙara biyan ko sisi ba. Sai dai a sake tsarin kwangilar ta yadda gwamnati za ta ƙaru, kuma a sassauta farashi yadda talaka zai iya sayen gidan idan an gina.
Kuma ya nuna rashin jin daɗin yadda aikin ya ɗauki tsawon shekaru 9, amma har yau ko rabin-rabi ba a kammala ba
Sai ya ce gwamnati ba za ta riƙa bayar da kwangila haka kawai don burga ko burgewa ba.
“Za mu riƙa bayar da kwangilar da muka tabbata cewa za mu iya kammalawa kafin mu bayar da wata,” inji Wike.
Jinjinar Wike Ga Rundunar Rusau A Abuja:
Minista Wike ya yada zango a Kabusa Junction, inda ya duba aikin rushe ƙananan rumfuna da ‘yan bukkokin da marasa galihu su ka giggina a matsayin matsugunan su.
Ya ce rushe wurin ya yi daidai, domin hukumar FCT Abuja ba za ta bar ɓatagari su riƙa addabar jama’a da takura masu ba. Ya ce duk ginin da aka yi ba bisa ƙa’ida ba, to a rushe shi kawai.
Discussion about this post