Yayin da ake jiran zuwan ranar Litinin domin rantsar da Janar Brice Nguema a matsayin sabon Shugaban Ƙasa a Gabon, PREMIUM TIMES Hausa ta binciko wasu muhimman batutuwa 20 dangane da babban sojan. Ciki kuwa har da batun dangantaka ta jini tsakanin sa da hanɓararren Shugaban Ƙasa, Ali Bango.
1. Jaridun ƙasar Gabon sun riƙa buga bayanan cewa Ali Bongo da Brice Nguema ‘yan uwan juna ne, ɗan mace da ɗan namiji su ke. Wato dai kakar su ta wajen uwa ɗaya kenan.
2. Brice Nguema shiga aikin soja, inda aka fara tura shi Makarantar Sojoji ta Royal Military Academy da ke Meknes, cikin Morocco ya samu horon zaratan sojojin tsaro.
3. Nguema ya zama Dogarin Kwamandan Kwamandan Dakarun Tsaron Shugaban Ƙasa, a lokacin mulkin Omar Bongo, mahaifin Ali Bongo da hamɓare a ranar Laraba.
4. Bayan mutuwar Omar Bongo cikin 2009, ɗan sa Ali Bongo ya hau mulki, kuma ya tura Brice Nguema ƙasashen Morocco da Sanagal ya yi aikin diflomasiyya.
5. Ya zama Babban Kwamandan Zaratan Tsaron Ƙasa, ‘Republican Guards’, a cikin 2019.
6. A matsayin sa na Babban Kwamandan Dakarun Tsaron Shugaban Ƙasa, waɗannan sojoji ne su ka fi ƙarfi a Gabon.
7. Mahaifin Brice Nguema jami’in soja ne.
8. Brice Nguema ne ya tsare ƙasar Gabon, ya hana duk wani motsin da zai kawo wa Ali Bongo cikas a cikin gida, a tsawon shekarun da ya yi ya na mulki.
8. Janar Brice Nguema hamshaƙin ɗan kasuwa ne, kuma attajirin gaske.
9. Ya na daga cikin ƙasaitattun attajiran Gabon da ake magana.
10. Binciken Ƙungiyar Fallasa Masu Laifuka Da Wawurar Kuɗaɗe ta OCCRP, wato ‘Organised Crime and Curruption Report’ cikin 2020, ta fallasa cewa Nguema ya sayi kantama-kantaman gidaje uku a Amurka.
11. Gida ɗaya da ya saya, ya mallake shi ne a unguwar masu hali birnin Maryland, Amurka.
12. Gidan ɗaya kuma unguwa matsakaitan masu hali, wato Hyattasville.
13. Gida na uku da Nguema ya saya, ya na cikin unguwar ya-ku-bayi, ta Silver Spring, duk a Maryland, Amurka.
14. An tambaye shi batun gidajen na sa uku, sai ya amsa wa ɗan jarida da cewa, “gidaje na dai sirri na ne, ba sirrin wani ba. Kowa kuwa da na sa sirrin. Kai ma ka na da na ka, ehe!”
15. A jawabin da ya yi lokacin da ya kifar da gwamnatin ɗan uwan sa Ali Bongo, Nguema ya ce, “Bongo ba shi da haƙƙin da zai sake yi shugabanci zango na uku. Saboda kowa ya san ya na fama ciwon shanyewar ɓarin jiki tun 2018, amma kuma kowa ba ya yin maganar.
16. “Bongo ya tattake Dokar Ƙasa da har ya nemi sake tsayawa zango na uku. Aka yi zaɓen kuma cike da murɗiya da maguɗi.
17. Dalili kenan muka taka masa burki, domin mu zo mu saisaita komai, sannan mu maida mulki a hannun farar hula.
18. Irin yanayin juyin mulkin da Janar Abdourahmane Tciani na Nijar ya yi wa Mohammed Bazoum, irin sa ne Janar Brice Nguema ya yi wa Ali Bongo. Su biyu ɗin duk su ke da haƙƙin tsaron shugabannin da su ka hamɓare.
19. A cikin ƙasar Gabon jama’a sai murna su ke yi an raba su da mulkin gidan Bongo na tsawon shekaru 56 da sunan dimokraɗiyya. Amma a ƙasashen ƙetare sai tir ake wa Sojojin Juyin Mulkin Gabon, saboda sun kifar da gwamnatin farar hula.
20. Nguema ya ce sun sauke Ali Bongo daga mulki, ba abin da za a yi masa. Kuma zai ci gaba da rayuwar sa a tsanake cikin lumana, kamar sauran ‘yan ƙasar Gabon.
Discussion about this post